Gwamna Da Kan Shi Ya Jawo Jama'a Zuwa Sallar Ruwa Saboda Yankewar Damina
- Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed ya tura wakilci wajen sallar rokon ruwa da aka shirya a jiya
- Auwal Jatau ya wakilci gwamnan a wajen ibadan matsayin na mataimakin gwamnan jihar Bauchi
- Dinbin mutane sun halarci sallar da Na’ibin limamin garin Bauchi, Ahmad Inuwa-Na’ibi ya jagoranta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Bauchi - Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed na jihar Bauchi, ya jagoranci mutane a wurin sallar rokon ruwa a ranar Alhamis.
Daily Trust ta tabbatar da cewa Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi yana cikin wadanda su ka bi wannan sallah ta musamman.
Da yake jawabi bayan an idar da sallar, Bala Abdulqadir Mohammed ya ce sun dade su na sa ran ruwan sama a har yanzu bai sauko ba.
Jama'a sun komawa Allah (SWT)
Ganin halin da aka shiga, Gwamnan ya ce al’ummar jihar Bauchi su ka dukufa wajen rokon Allah (SWT) domin ya sauko da ni’imarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamna Bala Mohammed ya yi kira ga mutane su cigaba da addu’o’i domin manoman Bauchi su ci moriyar daminar shekarar bana.
Auwal Jatau ya wakilci Gwamna
The Nation ta ce Mataimakin Gwamna, Auwal Jatau ya wakilci Gwamnan a wajen sallar.
Auwal Jatau ya yabawa Mai martaba Sarkin Bachi, Rilwanu Adamu da sauran malaman addinin musulunci da su ka shirya sallar rokon.
A jawabinsa, Jatau ya ce gwamnatinsu ta kawo tsare-tsare da su kawo cigaba tun daga saida taki da araha zuwa samar da tsaro a noma.
Na’ibin limamin garin Bauchi, Ahmad Inuwa-Na’ibi ya jagoranci sallar, Sakataren gwamnati, Ibrahim Kashim da daruruwa sun halarta.
Ana kuka a wasu garuruwa
Legit.ng Hausa ta fahimci an fara kiran a yi irin wadannan salloli a garin Kano. A Borno kuwa sai da Shehu ya jagoranci sallar rokon ruwa.
Zanna Bukar Guzamala mutumin Borno ne, ya fadawa Legit.ng Hausa tun bayan sallah, sau daya aka yi ruwa, kayan gona suna ta lalacewa."
"Ruwa ya tsaya tun bayan sallah, amma da Shehu Borno ya jagoranci sallah, an samu ruwa a was wurare a jiya (ranar Alhamis).
Shehu ya umarci Hakimai su cigaba da yin wannan roko a kasashensu. Kuma ko ina su na yi.”
- Zanna Bukar Guzamala
Asali: Legit.ng