Tallafi: Ko Wace Jiha Ce Za Ta Raba Kudaden Rage Radadi Ga Al'ummar Ta, NEC Ta Yi Bayani
- Majalisar Tattalin Arziki (NEC) ta samu matsaya kan yadda za a raba kudaden rage radadin cire tallafi
- Majalisar ta amince da ba wa jihohi don raba kudaden ta amfani da rijistar al'ummar jihohin su da suke da shi
- Sai dai wasu daga cikin mahalarta taron sun kushe tsarin inda suka ce ta yaya za a samu sahijiyar rijista a jihohin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta bayyana cewa ko wacce jiha ita za ta raba kudin rage radadin cire tallafi da Shugaba Bola Tinubu zai bayar.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun shi ya bayyana haka a jiya Alhamis 20 ga watan Yuli a Abuja yayin taron da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranta.
Taron ya samu halartar dukkan gwamnoni 36 na kasar da sauran masu ruwa da tsaki a Bankin Duniya da sauran manyan mutane, Daily Trust ta tattaro.
Cire Tallafi: Gwamnati Ta Yi Niyyar Saukakawa Mutane Rayuwa, Za Ta Sauya Amfani Da Fetur Zuwa Wani Abu
Yadda gwamnonin jihohi za su rarraba kudaden tallafin ga jama'a
Abiodun yayin ganawa da 'yan jaridu ya ce ko wace jiha za ta raba kudaden ta hanyar yin amfani da rijistar 'yan jihar da suka dace.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce wannan kara kudin man fetur ba yin Gwamnatin Tarayya ba ce kawai yanayin kasuwa ce tunda gwamnati ba ta saka hannu akan farashin, Tribune ta tattaro.
Ya kara da cewa za a biya kudin na tsawon watanni shida ba tare da haraji ba.
A jawabinshi, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce gwamnati za ta samar da bas bas masu amfani da wutar lantarki guda 10,000 don saukakawa al'umma.
Soludo ya soki yin amfani da rijista wurin raba kudaden
Da yake jawabi, gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya ce ta yaya za a tura wadannan kudade ga talakawa da ke cikin matsi wadanda mafi yawansu ba su asusun banki.
Ya ce majalisar ta amince da ba wa jihohi damar amfani da rijistar marasa karfi da kuma wadanda suka dace don raba kudaden cikin sauki, cewar The Guardian.
Ya ce:
"Ya kamata mu sani cewa ba mu da wata rijistar al'umma sahihiya a jihohin mu."
Shehu Sani Ya Fadi Abin Da Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Yi Kafin Karbar Tallafin Rage Radadi Na Tinubu
A wani labarin, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya ya shawarci mutane akan abin da za su yi kafin karbar kudin tallafin.
Sani ya soki yawan kudaden inda ya ce babu inda za su je kuma ba zai rage komai ba a radadin da ake fada.
Ya kara da cewa hakan almajirantar da kasa ce, inda ya ce wadanda suka karba a baya ma talauta su ya kara yi.
Asali: Legit.ng