Kona Qur'ani: Iraqi Ta Yi Barazanar Raba Gari Da Sweden, Ta Fadi Dalilai

Kona Qur'ani: Iraqi Ta Yi Barazanar Raba Gari Da Sweden, Ta Fadi Dalilai

  • Kasashen Musulmi da dama sun yi Allah wadai da kona Qur'ani a kasar Sweden a ranar babbar salla
  • Har ila yau, mutane dai-daiku sun nuna bacin ransu akan haka tare da kiran daukar mataki akan haka
  • Kasar Iraqi ta yi barazanar raba gari da Sweden Idan har aka sake kona Qur'ani a kasar kamar yadda ake yadawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Tun bayan kona Qur'ani mai girma a kasar Sweden, mutane da kasashe da dama ke Allah wadai da wannan aika-aika.

Kasar Iraqi ta bi sahu inda ta yi barazanar yanke alaka da Sweden Idan har aka sake kona Qur'ani a kasar.

Iraqi Ta Yi Barazanar Raba Alaka Da Sweden
Iraqi Ta Na Daf Da Raba Alakar Diplomasiyya Da Kasar Sweden Bayan Jita-jitar Sake Kona Qur'ani. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

Gargadin na zuwa ne bayan daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a ofishin jakadancin Sweden a birnin Baghdad bayan samun bayanan cewa za a sake aikata hakan a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: Da Ya Sha Suka, Tinubu Ya Janye Tsarin da Ya Yi Niyyar Fito da Shi

Iraqi ta yi barazanar raba alaka da Sweden

Ministan harkokin wajen Sweden ya ce ma'aikatansu na cikin koshin lafiya bayan zanga-zangar, inda ya ce Iraqi ta gaza wurin ba su kariya, Daily Nigerian ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Firaministan Iraqi, Mohammed Shi'a Al-Sudani ya yi Allah wadai da kona ofishin jakadancin Sweden inda ya ce za su kare faruwar hakan a gaba, The Guardian ta tattaro.

Amma kuma ya gargadi Sweden da cewa idan aka sake kona Qur'ani kamar yadda ake yadawa, za su dauki matakin yanke alaka da kasar, cewar Vanguard.

Sarki Musulmi ya yi Allah wadai da wannan aika-aika

Sarki Musulmi a Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar a na shi bangaren ya yi Allah wadai da wannan aika-aika.

A cikin sanarwar da ya fitar ya kirayi Sweden da ta zakulo wadanda suka aikata hakan don daukar mataki.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

Har ila yau, kungiyar limaman majami'u a Arewacin Najeriya suma sun nuna bacin ransu akan wannan ta'asa a kasar Sweden.

Kungiyar ta roki Musulmai da su kai zuciya nesa tare da tabbatar musu da cewa a shirye suke su kare martabar Qur'ani a ko da yaushe.

Sweden: Sarkin Musulmi Ya Yi Allah Wadai Da Kona Qur’ani, Ya Ce Ba Za Su Lamunta Ba

A wani labarin, Sarkin Musulmi a Najeriya, Sultan Sa'ad Abubakar ya yi Allah wadai da kona Qur'ani a kasar Sweden.

Sultan ya ce wannan aika-aika da aka yi a Sweden cin zarafi ne da kuma neman tsokana.

Ya yi kira da a dauki mataki akan wannan ta'asa don dakile faruwar hakan a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.