Dan Takarar Majalisar Tarayya A Kogi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Dan takarar majalisar Tarayya a mazabar Kabba-Bunu Ijumu da ke jihar Kogi, Cif Olaiya Michael Olobatoke ya riga mu gidan gaskiya
- Marigayin ya nemi takarar kujerar majalisar a karkashin jam'iyyar PDP a babban zaben da aka gudanar a farkon wannan shekara
- Iyalan mamacin sun tabbatar da rasuwar tasa inda suka wallafa a shafinsa na Facebook da cewa ya rasu a ranar Laraba 19 ga watan Yuli a Abuja
Jihar Kogi - Dan takarar majalisar Tarayya a jam'iyyar PDP a jihar Kogi Honarabul Olaiya Michael ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin ya nemi takarar mazabar Kabba-Bunu Ijumu a majalisar a babban zaben da aka gudanar a 2023, Legit.ng ta tattaro.
Marigayin ya rasu ne a jiya Laraba 19 ga watan Yuli a babban birnin Tarayya, Abuja.
Iyalan mamacin sun tabbatar da haka shafinsa na Facebook a yau Alhamis 20 ga watan Yuli.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar ta bayyana rasuwar dan majalisar a Abuja
A cewar sanarwar:
"Cikin alhini da godiya ga Ubangiji, muna bakin cikin sanar da mutuwar dan uwanmu, aboki kuma shugabanmu Cif Olaiya Michael Olobatoke (OMO).
"Ya rasu a jiya Laraba 19 ga watan Yuli a babban birnin Tarayya, Abuja."
Babu wani cikakken bayani akan musabbabin mutuwar tasa har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.
Olaiya ya zo na uku a zaben da aka gudanar da kuri'u 10,967 yayin da Salman Idris na jam'iyyar ADC ya ci zaben da kuri'u 13,867, cewar Tribune.
Marigayin ya godewa mazabarsa da irin gudumawar da suke ba shi
Bayan faduwa zaben, marigayin ya mika godiyarsa ga mazabarsa saboda irin goyon baya da suka nuna masa tun yakin neman zabe har zuwa karshe.
Shehu Sani Ya Lissafa Manyan Dalilai 2 Da Suka Yi Sanadiyar Ficewar Adamu Daga Matsayin Shugaban APC Na Kasa
Tun farko, Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana sakamakon zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Hakan na zuwa ne bayan 'yan takarar jam'iyyun ADC da APC mai mulki sun kusa yin kunnen doki wanda babu wata rata a tsakanin kuri'un da suka samu.
Yayin neman zabe, Olaiya ya yi alkawarin tabbatar da tsaro da kuma hadin kai a tsakanin jama'ar da ke mazabarsa.
Ya ce:
"Tabbas babu abinda zan iya cewa akan yadda kuke nunamin goyon baya irin haka.
"Nagode matuka da wannan mutuntawa kuma ba zan taba mantawa da hakan ba."
Mahaifiyar dan majalisa da ke takarar kujerar kakakin majalisa ta rasu
A wani labarin, mahaifiyar dan majalisa mai wakiltar mazabar Chachanga a jihar Niger, Umar Bago ta rasu.
Marigayiyar, Aisha Mohammed ta rasu ne a ranar 1 ga watan Mayun 2022 bayan gajeriyar jinya.
Sanarwar ta kara da cewa za a yi sallar jana'izarta a ranar Lahadi 2 ga watan Mayu kamar yadda Musulunci ya koyar.
Asali: Legit.ng