Yanzu Yanzu: Mahaifiyar dan majalisa da ke takarar kujerar kakakin majalisa ta rasu

Yanzu Yanzu: Mahaifiyar dan majalisa da ke takarar kujerar kakakin majalisa ta rasu

- Wani dan majalisar wakilai, Umar Bago, yayi rashi na mahaifiyarsa

- Bago wanda ke takarar kujerar kakakin majalisar wakilai ya rasa mahaifiyarsa a ranar Asabar, 1 ga watan Yuni

- Za a binne Hajiya Aisha a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, bayan sallar Janaizah a Minna, jihar Niger

Hajiya Aisha Mohammed, mahaifiyar wani dan majalisar wakilai da ke takarar kujerar kakakin majalisa kuma mamba mai wakiltan mazabar Chanchaga na jihar Niger, Umar Mohammed Bago, ta rasu.

Wani jawabi da aka aike ma Legit.ng dauke da sa hannun Hon. Victor Afam Ogene, kakakin kungiyar kamfen din Mohammed Bago, yace Hajia Aisha ta rasu a ranar Asabar, 1 ga watan Mayu bayan yar gajeriyar rashin lafiya.

“Cikin godiya ga Allah muna fatan sanar da rasuwar Hajia Aisha Mohammed, mahaifiyar wanda muke burin zai zama kakakin majalisa kuma mamba mai wakiltan mazabar Chanchaga na jihar Niger a majalisar wakilai, Hon. Mohammed Bago," cewar sanarwar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai wa Rochas Okorocha hari har gida

Sanarwar yace za a kuma bine Hajiya Aisha a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni bayan Sallar Janaizah a Minna, jihar Niger, daidai da koyarwar addinin Musulunci.

Sarwar ya kuma yi addu’an Allah “ya yafe mata sannan ya bata Aljannatul Firdaus”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel