Muna Dab Da Durkushewa, Dillalan Mai Sun Koka, Sun Bayyana Irin Halin Kuncin Da Suke Ciki Bayan Cire Tallafi

Muna Dab Da Durkushewa, Dillalan Mai Sun Koka, Sun Bayyana Irin Halin Kuncin Da Suke Ciki Bayan Cire Tallafi

  • Tun bayan cire tallafin mai a Najeriya, 'yan kasar suke cikin mawuyacin hali na tsadar mai a kasar
  • Ana cikin haka sai ga karin farashin man daga N540 zuwa N630 a wasu gidajen man kasar
  • Wasu daga cikin dillalan man da kuma masu siyarwa sun koka kan yadda hakan ke gurgunta kasuwancinsu

FCT, Abuja - Kungiyar Dillalan Man Fetur (IPMAN) ta ce tashin farashin mai a kasar na barazana ga harkokin kasuwancinsu.

Shugaban kungiyar a jihar Enugu, Anyaso Chinedu ya ce kasuwarsu ta fadi da kusan kashi 50 tun bayan cire tallafi a watan Mayu.

Muna Dab Da Durkushewa, Dillalan Mai Sun Bayyana Irin Halin Kunci Da Suke Ciki Bayan Cire Tallafi
Tun Bayan Da Shugaba Tinubu Ya Cire Tallafin, Mutane Ke Kokawa Irin Halin Kunci Da Suke Ciki. Hoto: Facebook.
Asali: Facebook

Ya ce yanayin rashin ciniki saboda tashin farashi ya fara shafar al'amuransu na yau da kullum, Premium Times ta tattaro.

Yadda tsadar mai ke son gurgunta dillalan mai

Chinedu ya ce tabbas idan ba a dauki matakin kawo gyara ba 'yan kasuwa da dama za su ruguje kuma hakan zai sa rasa miliyoyin ayyuka a kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu: COEASU Ta Umarci Mambobinta Su Na Zuwa Aiki Na Kwanaki 2 Kadai A Sati Bayan Cire Tallafi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa wannan cire tallafi su yafi shafa saboda yawan ribar da suke samu a baya ta ragu da kashi 50, Daily Trust ta tattaro.

A cewarsa:

"Mafi yawan dillalan na cikin mawuyacin halin da za su iya barin kasuwar bayan biyan ma'aikata ga kuma sabbin dokoki daga bankuna.
"Muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta samar da mafita na rage farashin litar mai don ceto albarkatun mai.

Mafi yawan gidajen mai sun koka kan tsadar mai da kuma rashin ciniki

A wasu gidajen mai da wakilin Legit.ng Hausa ya bincika, ana siyar da litar mai N620 zuwa N630.

Gidajen mai na Ummodah da Lelewal da kuma LB suna siyar da lita akan N620, yayin da Jiri Brothers da wasu ke siyarwa akan N630.

Daya daga cikin masu siyar da mai Gombe, Abdullahi Jungudo ya bayyana yadda farashin ya shafi harkar cinikayya a man fetur din.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Tsare Wani Matashi Dan Kwaya Da Ake Zargin Ya Shake Wuyan Mahaifiyarsa Har Lahira

Ya ce:

"Kasan wannan farashi yanayin kasuwa ce ta ke juyawa, amma tabbas hakan na shafar harkar kasuwancinmu.
"Iya tsadar mai din iya rashin ciniki a wurinmu, idan kuma ya sauka muna dan samun ciniki sosai."

A wasu wurare a jihar Lagos ana siyar da litar mai akan kudi N610, kamar yadda wani ya bayyana wa Legit.ng Hausa.

Rashin Ciniki Da Tarun Matsalolin Da Suke Shafar Masu Gidajen Mai Bayan Cire Tallafi

A wani labarin, masu gidajen mai sun koka kan yadda cire tallafin mai ya shafe su a harkar kasuwa.

Mafi yawa daga masu gidajen mai din sun bayyana wa Legit.ng Hausa cewa ba mutane kadai ba ne fa abin ya shafa.

Suka ce idan aka kwatanta da baya yanayin cinikin da suke ya bambanta sosai da na yanzu wanda hakan barazana ne ga kasuwancinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.