Jerin Jihohin Da Suka Bayar Da Hutu a Ranar Laraba Domin Zagoyowar Shekarar Musulunci

Jerin Jihohin Da Suka Bayar Da Hutu a Ranar Laraba Domin Zagoyowar Shekarar Musulunci

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na III ya sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin 1 ga watan Muharram na shekarar 1445 bayan Hijirah.

Sanarwar hakan ta biyo rashin ganin jinjirin watan Muharram a ranar Litinin 29 ga watan Dhul Hijjah wanda hakan ya sanya ranar Talata ta zama 30 ga watan Dhul Hijjah na shekarar 1444 bayan Hijirah.

Jihohin da suka bada hutu domin zagoyowar sabuwar shekarar musulunci
Jihohin sun sanar da ranar Laraba a matsayin ranar hutu Hoto: Dauda Lawal/Governor Seyi Makinde/Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Biyo bayan wannan sanarwar da Sarkin musulmin ya fitar, jihohi da dama sun sanar da ranar Laraba a matsayin ranar hutu a jihohinsu.

Ga jerinsu kamar haka:

Sokoto

Jihar Sokoto ta ssnar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar domin zagayowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445.bayan Hijirah.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Sabuwar Shekarar Musulunci: Gwamnan PDP Ya Bayyana Ranar Laraba a Matsayin Ranar Hutu a Jiharsa

Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na gwamnan jihar, Malam Bawa Abubakar ya fitar, cewar rahoton Leadership.

Osun

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya taya al'ummar Musulmai murnar zagayowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.

Gwamnan ya kuma bayyana ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci, cewar rahoton Vanguard.

Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya bi sahun gwamnonin da suka bayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu domin shigowar sabuwar shekarar musulunci.

Gwamnan ya bayyana cewa sanarwar hakan ta biyo bayan bayyana ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin 1 ga watan Muharram, 1445 da mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi.

Zamfara

Jihar Zamfara kamar yadda aka saba a al'adance tana bayar da hutu a duk ranar 1 ga watan Muharram na shekarar musulunci domin murnar zagayowar sabuwar shekarar musulunci.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP Ya Ayyana Ranar Laraba a Matsayin Ranar Hutu, Ya Bayyana Dalili

A wannan karon ma gwamna Dauda Lawal Dare ya bayar da hutun inda ya bayyana ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihar.

Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da bayar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.

Haka kuma shugaban ma'aikatan jihar, Hussaini Ali Kila, ya buƙaci ma'aikatan jihar da su yi amfani da ranar wajen yi wa jihar da ƙasa baki ɗaya addu'ar samun ci gaba mai ɗorewa a shekarar.

Jihohin Kwara da Oyo

Gwamnonin jihohin Kwara da Osun su ma sun bi sahun wasu daga cikin takwarorinsu wajen bayyana ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu a jihohinsu.

Gwamnonin sun buƙaci al'ummar Musulmai da su yi amfani da lokacin wajen yin addu'o'i ga jihohin da ƙasa baki ɗaya.

Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Kan Kona Al-Qur'ani a Sweden

Kara karanta wannan

Sarkin Gombe Ya Nada Tsohon Kwamishina a Matsayin Sabon 'Sarkin Malaman Gombe'

A wani labarin kuma mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya yi Allah wadai da ƙona Al-Qur'ani da aka yi a ƙasar Sweden.

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana hakan a matsayin babbar aika-aika da cin zarafi da neman tsokanar al'ummar Musulmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng