Doguwar Matar da Tsawonta Ya Kusan Taba 'CeilinG' Ta Ba da Mamaki a Wani Bidiyo, Jama’a Na Ta Cece-Kuce

Doguwar Matar da Tsawonta Ya Kusan Taba 'CeilinG' Ta Ba da Mamaki a Wani Bidiyo, Jama’a Na Ta Cece-Kuce

  • Wata kyakkyawar mata mai tsayin gaske ta yadu a kafar sada zuumunta, mutane da yawa sun yi mamakin irin baiwar da Allah ya yi mata na tsawo
  • Matar mai suna Gbane Mandjalia ta yada wani faifan bidiyo don nuna tsayinta a kafar TikTok, kuma ya ya yadu ainun inda mutane samda 940.5k ke magana a kai
  • Mabiyanta da suka ga tsayinta sun kadu, yayin da wasu suka bayyana mamakin cewa mutum zai iya yin wannan tsawon dama a rayuwa

Wata doguwar mata wacce ke da tsayi mai ban sha'awa ta yadu a kafar sada zumunta bayan da ta yada wani gajeren bidiyonta a TikTok.

Kyakkyawar matar mai suna Gbane Mandjalia tana cikin daki ne a lokacin da ta dauki bidiyon, sai mutane suka lura cewa kanta ya kusa taba silin.

Kara karanta wannan

“Kana Da Karfin Hali”: Malamar Jami’ar Najeriya Ta Fashe Da Kukan Murna Yayin da Dalibinta Ya Nemi Aurenta a Bidiyo

Bidiyon ya nuna asalin tsawon Gbane, kuma tsayin na ta ya bayyana a matsayin abin mamaki ga duk wanda ya kalli bidiyon.

Yadda wata doguwar mace ta sanya mutane cikin mamaki
Hotunan matar da tsawonta ya kai silin | Hoto: @gbanemandjalia.
Asali: TikTok

Doguwar mace mai dogayen kafafu ta burge jama’a a TikTok

Daya daga cikin abinda ya ja hankalin mabiyan Gbane zuwa ga martani a faifan bidiyon shine dogayen kafafunta. Kafafunta sun yi tsayi har ya zama abin da aka fi gani na daukar hankali matuka a jikinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda aka ganta, Gbane na sanye ne da wata karamar riga mai yankakken gefe wacce ta kama jikinta tare da bayyana surarta.

Haka nan kuma, ta sa wasu takalmi masu tsini da ke nuna karin tsawo gare ta, wanda mata da yawa suka fi sha’awar sanya wa. Da yawa daga cikin mabiyanta sun nuna ta burge su.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Bayan ganin bidiyon, mutane da yawa sun bayyana martaninsu game da wannan matar da ba a saba ganin mai irin tsawonta ba. Ga kadan daga ciki:

Kara karanta wannan

“Yanzu Na Mallaki Gidan Kaina”: Budurwa Ta Ginawa Kanta Karamin Gida a Shekaru 19, Hotunan Sun Yadu

@Toothfairy:

"Me yasa bata zama ‘yar wasa ba? Ni dai na gudu? Wayyo Allah na."

@sexynayaray:

"Ashe dogayen 'yan mata za su iya sanya takalmi mai tsini? Ina tambaya ne ga kawata."

@Lobbeuh236:

"Abin da muke kira mutum ke nan, mu mutane ne."

@raphael_edwin:

"Sarauniya mai tsayi."

@Money:

"Kuma a haka kika sanya takalmi mai tsini wow.”

@samuel.etoh:

"Ki bari su numfasa kadan mana, kada ku shake su."

@sengibychefcoco:

"Ina fatan dai tana sana’ar gwada kayan kwalliya domon na ga ta cancanta.”

Mace mafi tsawo a duniya: Rumeyasa Gelgi 'yar kasar Turkiyya

A bangare guda, kundin tarihin Guiness World Records ya tabbatar da cewa wata mata mai shekaru 24 'yar kasar Turkiyya ne mace mafi tsawo a duniya a halin yanzu.

A cewar Guiness World Records, Rumeysa Gelgi ta lashe kambun ne da tsawon 215.16cm (7ft 07in) kamar yadda ya zo a ruwayar BBC Pidgin.

Kara karanta wannan

Yadda Hoton Rahama Sadau Da Wani Farin Fata Ya Haddasa Cece-Kuce a Soshiyal Midiya

An sake gwada tsawon Rumeysa a wannan shekarar, bayan an fara bata kambun mace yar kasa da shekara 19 a 2014, a lokacin da ta kai shekaru 18, tsawonta ya kai 215.16cm (7ft 0.7in) a lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel