Shehu Sani Ya Ce Rufe Iyakokin Kasa Bai da Amfani, Ya Kushe Shirin Tinubu Kan Wadatar da Abinci
- Tsohon sanata a Najeriya ya hangi matsala game da shirin Tinubu na wadatar da ‘yan Najeriya da abinci, inda yace yaudara ce
- Ya kuma bayyana cewa, ‘yan ta’adda na kashe manoma, don haka samar da abinci ke da wahala a kasar nan
- Ya kuma kushe yadda gwamnatin Buhari ta yi amfani da damar nuna wa duniya an yi noman wadataccen abinci a kasar nan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Tsohon sanata daga jihar Kaduna, Shehu Sani ya yiwa gwamnatin Tinubu da ta Buhari kudin goro game da dokokinsu.
Sanatan ya bayyana cewa, yaudara ce kawai ci gaba da rufe iyakokin kasa da aka yi tare da hana shigo da abinci cikin kasar nan.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da kokawa kan yadda tsadar rayuwa ta yi yawa a kasar ga kuma tsadar man fetur.
Martanin sanata Shehu Sani ga yunkurin Tinubu na samar da wadataccen abinci
Da yake martani ga tsare-tsaren Tinubu, Shehu Sani ya ce tabbas an yaudari ‘yan Najeriya a mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, dalar shinkafa aka nuna ba komai bane face cika ido don yaudarar ‘yan kasar da nuna wa duniya an wadatda abinci.
Ya bayyana hakan ne tare da kushe aniyar Tinubu ta sanya dokar ta baci game da wadatar abinci a Najeriya.
Hakazalika, ya bayyana damuwa game da yadda ‘yan ta’adda ke kashe manoma tare da kakaba musu haraji kan guminsu.
“Ba za ku samun wadatar abinci ba a kasar da 'yan ta'adda ke kashe manoma da kuma tilasta wa manoman biyan haraji ga 'yan bindiga ba.
“Alanta dokar ta baci kan tabarbarewar wadatar abinci ta fallasa yaudara game da waccar dalar shinkafar da kuma rashin fa’idar garkame iyakokin kasa.”
Shugaba Tinubu ya ayyana ta baci kan samar da abinci a Najeriya
A wani labarin, shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana ta baci kan tsamar da isasshen abinci a Najeriya.
Kakakin shugaban kasa, Dele Alake ne ya bayyana haka yayin zantawa da masu dauko rahoton gidan gwamnati ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, 2023.
Shugaban kasan ya bada umarnin cewa duk wasu batutuwa da suka shafi abinci da samar da ruwan sha da sauke farashi a maida su karkashin kulawar majalisar tsaro ta kasa.
Asali: Legit.ng