Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnonin Edo, Imo da Ebonyi Sun Kara Albashin Ma’aikata
- Cire tallafin man fetur a Najeriya ya jefa 'yan kasar da dama cikin wahala, kadan daga ciki akwai tsadar sufuri, hauhawar farashin kayayyaki, da karin kudin gudanar da rayuwa
- Dangane da hakan, wasu gwamnoni sun aiwatar da matakan da suka dace don rage radadin hakan, kamar dai karin albashin ma’aikatan gwamnati
- Wasu gwamnonin jihohin kasar sun sanar da karin albashi domin rage radadin da ake ciki na cire tallafin man fetur
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
‘Yan Najeriya da dama na fuskantar karin wahalhalu sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin Najeriya ta yi, lamarin da ya jawo tsadar sufuri da hauhawar farashin kayayyaki da kuma tsadar rayuwa.
Yayin da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana wasu matakai na kwantar da hankali domin dakile tasirin cire tallafin, wasu gwamnonin jihohi ma sun kara albashin ma’aikatansu.
Ga jerin gwamnonin da suka bayyana karin albashin ma’aikatansu.
1. Gwamnatin Ebonyi ta kara albashin ma’aikata da N10,000
Gwamna Francis Ogbonna Nwifuru na jihar Ebonyi ya bayar da umarnin a kara Naira 10,000 ga albashin ma’aikatan gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, gwamnan ya bayar da umarnin ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jihar a Centenary, Abakaliki.
2. Gwamnan Imo Uzodimma ya karawa ma'aikata albashi
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya kuma sanar da karin albashin da N10,000 ga ma’aikatan jihar domin dakile radadin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Otal din Rockview Owerri a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli.
3. Obaseki ya kara mafi karancin albashi, ya rage kwanakin aiki zuwa uku a mako
Hakazalika, gwamnatin jihar Edo ta taimakawa ‘yan jihar dangane da cire tallafin man fetur, wanda ya haifar da tashin gwauron zabi na kayayyaki.
Gwamna Godwin Obaseki a ranar Talata, 6 ga watan Yuni, ya bayyana cewa a yanzu ma’aikatan gwamnati za su koma aikin kwanaki uku a maimakon kwanaki biyar a mako, saboda karin kudin sufuri.
Haka nan, gwamnan ya ce ya kara N10,000 kan N30,000 na karancin albashi da ake biyan ma’aikatan jihar.
Kwamitin rabon kayan tallafi na shugaba Tinubu ya fitar da sabbin bayanai masu muhimmanci
A wani labarin, kwamitin rabon kayan tallafi kan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya kafa, ya gudanar da taro a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli a birnin tarayya Abuja.
A cewar rahoton Premium Times, gwamnonin Bauchi, Bala Mohammed, Charles Soludo na jihar Anambra, Uba Sani na jihar Kaduna da Hyacinth Alia na jihar Benue, da wakilan kungiyoyin kwadago sun halarci taron.
Shugaban kwamitin rabon kayan tallafin, gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya bayyana cewa ana ci gaba da shirye-shirye domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur din ga 'yan Najeriya.
Asali: Legit.ng