Yan Sandan Jigawa Sun Kama Likitan Bogi Da Ya Dade Ya Na Dura Wa Jama’a Gurbataccen Magani

Yan Sandan Jigawa Sun Kama Likitan Bogi Da Ya Dade Ya Na Dura Wa Jama’a Gurbataccen Magani

  • Jami’an ‘yan sandan jihar Jigawa sun cafke wani likitan bogi da ya dade yana cutar jama’a a birnin Dutse.
  • Wanda ake zargin David Samuel ya bude katafaren asibiti na musamman inda ya ke kula da marasa lafiya
  • Kakakin rundunar a jihar, DSP Lawan Shiisu shi ya bayyana haka inda ya ce an kama shi ne bayan samun bayanan sirri

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Jigawa – Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa tare da hadin gwiwar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun yi nasarar kama wani likitan bogi a jihar.

Wanda ake zargin mai suna Samuel David ya dade yana siyar da magani ba bisa ka’ida ba a cikin Dutse.

Jami'an ’Yan Sanda Sun Cafke Da Wani Likitan Bogi Da Ya Dade Ya Na Cutar Jama'a
Rundunar Ta Ce Samuel Ya Bude Katafaren Dakin Magani Da Yake Jinyar Mutane. Hoto: NTA News.
Asali: Twitter

Kakakin rundunar ‘yan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam shi ya bayyana haka inda ya ce an kama likitan bogin ne bayan samun bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Miji Da Mata Sun Yi Basajar Shiga Musulunci Yayin Da Suka Tafkawa Liman Sata a Yobe

Rundunar ta yi bayanin yadda ta kai samame dakin maganin

Ya ce rundunar su ta kai samame shagon da ya ke siyar da magani mai suna Shawai Medical Plus a Sabuwar Takur da ke birnin Dutse, NTA News ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin samamen, kakakin ya ce Samuel ya yi ikirarin shi likita ne da ke asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke birnin Dutse.

Yayin bincike a ofishin binciken laifuka na 'yan sanda a Dutse, likitan bogin ya na gudanar da ‘yar kwarya-kwaryar asibiti da ya ke ba da magani da kuma kula da marasa lafiya, cewar Independent.

An kama Samuel da takardun bogi da yake nuna shi likita ne

An samu Samuel da takardar shaidar kamala jami’ar Usman Danfodio University da kuma shaidar kamala bautar kasa sai kuma takardar shaidar zama mamba na Kungiyar Likitoci na Najeriya (NMA).

Kara karanta wannan

Jami’an Gwamnati Sun Dura Gareji, An Yi Awon Gaba da Motocin Tsohon Gwamna

Samuel ya tabbatar da dukkan tuhume-tuhumen da ake a kansa inda ya ce duk wadannan takardu na karya ne, ya kara da cewa an dade da korarsa daga jami’ar.

Rundunar ta tabbatar wa da jama’a cewa za a tura Samuel zuwa kotu da zarar an kamala binciken kwarai, cewar Daily Post.

Kotun A Kano Ta Daure Lauyan Bogi Watanni 15 A Gidan Kaso

A wani labarin, kotun shari'ar Musulunci ta gurfanar da wani lauyan bogi da ake zargi da damfara da kuma cin amana.

Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano ta na zargin Zaharadden Sani da ikirarin shi lauya ne.

An daure wanda ake zargin dan asalin jihar Kaduna watanni 15 a gidan gyaran hali, bayan ya sake ayyana kansa a matsayin dan jarida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel