Wasu Yan Najeriya Sun Cika Da Murna Yayin da Suka Ga Tsohon Shugaban Kasa Buhari Yana Jan Kafa a Titin Daura

Wasu Yan Najeriya Sun Cika Da Murna Yayin da Suka Ga Tsohon Shugaban Kasa Buhari Yana Jan Kafa a Titin Daura

  • Bidiyon tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana yawon motsa jiki a titin Daura ya bayyana
  • A bidiyon wanda tsohon hadimin tsohon shugaban kasar, Bashir Ahmad ya wallafa a soshiyal midiya, an gano wasu mata suna farin cikin ganinsa yayin da suke mika gaisuwarsu gare shi
  • Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakunansu a kan bidiyon,wasu sun yi masa fatan alkhairi sannan wasu kuma sun soke shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Daura, Katsina - Yan makonni bayan mika mulki ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, an gano wani bidiyon tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yana tafiya a titin Daura da ke jihar Katsina.

Bashir Ahmad, daya daga cikin hadiman tsohon shugaban kasar ne ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli.

Buhari yana tafiya a titin Daura
Wasu Yan Najeriya Sun Cika Da Murna Yayin da Suka Tsohon Shugaban Kasa Buhari Yana Jan Kafa a Titin Daura Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Idan za ku tuna, Buhari da matarsa, Hajiya Aisha sun koma mahaifarsa ta Daura da zama tun bayan da ya mika mulki ga shugaban kasa Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara da Kyau Amma Tun Farko na San Babu Inda Buhari Zai Je - Dattijon Arewa

A cikin bidiyon, an gano wasu taron jama'a da suka hada da mata, yara da wasu samari da suka cika da farin cikin ganin tsohon shugaban kasar, inda suka kasa boye mamakinsu na cewa yau ga su ga shi ido da ido.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An jiyo wata murya na cewa:

"Wallahi tallahi ga shi, ga Janar Muhammadu Buhari, yau ga mu ga Buhari. Allah mai iko. Allah mai iko ranka ya dade, Allah ya kara maka lafiya."

Sai dai tare da shi akwai wasu masu tsaronsa, wadanda suka sanya shi a tsakiya yayin da dandazon mutanen suka ci gaba da binsa a baya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani a kan bidiyon Buhari yana tafiya a titin Daura

@Muhamma53561171 ya yi martani:

"Duniya kenan yanzu ina mulkin yake shikenan fa sai dai ya jira tambaya Daga walakiri."

Kara karanta wannan

Yadda Hoton Rahama Sadau Da Wani Farin Fata Ya Haddasa Cece-Kuce a Soshiyal Midiya

@Ibrahim79117840 ya ce:

"Yayi Buhari kayi kokari harkar saida motsa jiki."

@misterbashir ya ce:

"Badaban darajar furfura ba, idona idon wannan mutumin sai na daddala masa mari ."

@basheedoomony11 ya ce:

"Kaga wannan Dan wahalan. Wlh bamu yafe ba Kuma wlh kadan ma kafara gani."

@MAbubakar36 ya ce:

"Buhari bawan Allah, Buhari me farin jini, Allah yasa ya gama da duniya lafiya (Ameen)."

@ABDULLA40520624:

"Allah ya cigaba da masa jagora."

@AbubakarMaraf17:

"Baba Buhari Jigon Nigeria .

"Uban Talakawa da marayu Allah ya Kara baka Nisan Kwana."

@realkata1:

"Allah ya kara lafiya Baba Buhari, wannan shine karshe mai kyau."

Ya tafi Landan jinya kamr yadda ya saba, Rafsanjani ya caccaki Buhari

A wani labarin kuma, Legit.ng ta kawo a baya cewa mai rajin kare yancin dan adam kuma dan fafutukar yaki da rashawa, Auwal Musa Rafsanjani ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana kasar Turai inda yake ganin likita kamar kullun.

Ku tuna cewa a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, Garba Shehu, tsohon hadimin Buhari, ya ce tsohon shugaban kasar ya tafi Landan saboda ya kaucewa hayaniya saboda baya jin dadin yadda mutane ke yi masa zarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng