Hafsan Soji Ya Ja Kunnen Gwamnonin Arewa Maso Yamma A Kan 'Yan Bindiga, Ya Fadi Kudirin Rundunar

Hafsan Soji Ya Ja Kunnen Gwamnonin Arewa Maso Yamma A Kan 'Yan Bindiga, Ya Fadi Kudirin Rundunar

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi fatali da maganan yi wa 'yan bindiga afuwa ko kuma yin sulhu da su
  • Shugaban hafsan sojin kasar, Manjo Janar Taoreed Lagbaja shi ya bayyana haka a Abuja yayin wata ganawa
  • Ya ce abin da rundunar ke bukata shi ne cire hannun gwamnonin yankin don barin jami'ansu su yi aiki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta ce babu wani afuwa ko sulhu tsakaninsu da 'yan bindiga musamman a Arewa maso Yamma.

Rundunar ta ce abin da take bukata kawai shi ne gwamnonin yankin Arewa masu Yamma su bar su su yi aikinsu.

Taoreed Lagbaja Ya Ja Kunnen Gwamnonin Arewa Maso Yamma A Kan 'Yan Bindiga
Shugaban Hafsan Soji Ya Bukaci Gwamnonin Arewa Maso Yamma Da Su Cire Hannunsu A Harkar Tsaro. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Rundunar ta gargadi 'yan bindigan da su yi gaggawar tserewa daga yankin kafin kunle ko wace kofa a fadin kasar.

Ya bukaci gwamnonin Arewa maso Yamma su bar su, su yi aikinsu

Kara karanta wannan

Yadda Hoton Rahama Sadau Da Wani Farin Fata Ya Haddasa Cece-Kuce a Soshiyal Midiya

Hafsan sojin kasar, Manjo Janar Taoreed Lagbaja shi ya bayyana haka a Abuja yayin karbar bakoncin gwamnan jihar Zamfara, Lawal Dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya roki gwamnonin yankin da su bar rundunar ta yi aikin ta don kawar da dukkan tsageran da ke yankunan, Daily Trust ta tattaro.

A cewarsa:

"Mai girma gwamna, ya kamata mu duba maganan sulhu din nan, tsageran nan ba sa son sauya wa, sulhu ne ya ke ba su daman shirya wa da sake kai hare-hare."

Wannan gargadi na zuwa ne bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani ya shawarci Shugaba Tinubu a kan yi wa 'yan bindigan afuwa.

A kwanakin baya Sanata Yerima ya nemi a yi sulhu da 'yan bindiga

Sanata Yerima ya roki shugaban kasa, Bola Tinubu da ya yi sulhu da 'yan bindigan da ke jihar Zamfara da sauran yankunan, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Tsawa Ta Yi Ajalin Masu Garkuwa Da Mutane 3 A Jihar Arewa

Inda ya ce wannan sulhu alkairi ne ganin yadda marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'adua ya yi wa 'yan Neja-Delta a lokacinsa.

Rundunar Soji Yi Gargadi Kan Masu Shirin Hana Bikin Rantsar da Tinubu

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta yi gargadi akan masu son ta da zaune tsaye yayin rantsar da Bola Tinubu.

Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri cewa akwai wadanda suke son kawo hargitsi yayin bikin rantsarwar.

Ta ce akwai wasu 'yan siyasa da fitattun a kasar da bayanan suka tabbatar da abin ke zuciyarsu, ta na gargadinsu da babbar murya a kan kudirinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.