“Naso Kawai Ace Na Yi Aure”: Jarumar Fim Ta Magantu a Kan Aurenta 2 Da Suka Mutu

“Naso Kawai Ace Na Yi Aure”: Jarumar Fim Ta Magantu a Kan Aurenta 2 Da Suka Mutu

  • Shahararriyar jarumar Nollywood, Funke Akindele, ta magantu a kan aurenta biyu da suka mutu
  • Yayin da take zantawa da kwararren dan jarida, Chude Jideonwo, Funke ta shawarci yan mata da kada su ga an matsa masu su yi gaggawan shiga gidan aure
  • A cewar jarumar fim din, kawai ta so ace ta yi aure sannan ta mallaki yara ne amma abubuwa basu tafi daidai ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fitacciyar jarumar nan ta Nollywood mai farin jini, Funke Akindele, ta shiga kanen labarai a soshiyal midiya bayan ta magantu kan mutuwar aurenta.

Ku tuna cewar jarumar fim din ta fara auren wani shahararren mutum, Kehinde Oloyede, sannan daga baya ta aure fitaccen mawaki Abdulrasheed ‘JJC Skillz’ Bello, amma duk auren suka mutu.

Yayin da take jawabi a wata hira da Chude Jideonwo, jarumar wacce ke da yara biyu ta magantu a kan mutuwar aurenta.

Kara karanta wannan

Sakataren APC Ya Jero Irin Mutanen da Shugaban Kasa Zai Dauko Su Zama Ministoci

Jaruma Funke Akindele ta gargadi yan mata a kan yin gaggawa a harkar aure
“Naso Kawai Ace Na Yi Aure”: Jarumar Fim Ta Magantu a Kan Aurenta 2 Da Suka Mutu Hoto: @funkejenifaakindele
Asali: Instagram

Funke ta gargadi yan mata da suke ganin an matsa masu don su yi aure. Ta shawarce su da su kwantar da hankalinsu saboda za su yi gaggawan fita idan har suka yi gaggawan shiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

"Dalilin kawai da yasa zan fada maki wannan don karfafawa yan mata da ke waje wadanda suka matsu yi aure, wadanda aka matsawa su yi aure gwiwa ne. Ku kwantar da hankalinku, ku dauki lokacinku, idan kika yi gaggawan shiga, za ki yi gaggawan fita."

Da take ci gaba da jawabi, Funke ta yi bayanin yadda ta so yin abun da ya dace ta hanyar da ya dace da yin aure da samun yara. Sai dai kuma, aurenta na farko ya mutu ta hanyar da bata dace ba.

A cewarta, ta gano cewa labarin mutuwar aurenta ya bazu a duniya lokacin da wata ta kirata tana wajen aiki. Funke ta bayyana cewa ta so ta mutu a lokacin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Sabuwar Cutar Mashako Da Ta Bulla a Jihar Yobe Ta Kashe Yara 30 Da Kwantar Da 42 a Asibiti

Jarumar ta yarda cewar ta rasa abubuwa da dama a wannan lokacin amma ta yanke shawarar cewa ba za ta bari ya kai ta kasa ba.

Kalamanta:

"Naso kawai ace na yi aure ne. Ina son yin abun da ya dace, samun yara shikenan. Da na fara yin aurena na farko, bai tafi daidai ba. Kuma ya mutu ta hanya mara dadi, a soshiyal midiya, hayaniyar ya karade koina. Ina daukar fim ne wata ta kira ni sannan ta fada mani, na so na mutu!
"Kun san na yi kuka, na rasa wasu harkoki masu tsoka a lokacin. Amma ban bari ya kai ni kasa ba."

Ta take ci gaba da bayani, jarumar wacce ta haifi tagwaye maza ta shawarci yan mata da su yi aure saboda suna so kuma saboda suna son abokin zamansu da son kare rayuwarsu da shi.

Ta kara da cewar bai kamata mutane su yi aure saboda yara ko saboda matsin jama'a ba lokacin da mutane za su fara yi masu shagube saboda basu haihu ba a wani shekaru.

Kara karanta wannan

Kwanaki 42 Akan Mulki, Gwamnatin Tinubu Ta Gagara Cika Babban Alkawari Da Ta Dauka Wa Yan Najeriya

Jama'a sun yi martani

Damilareolasupo165:

"Abun ba na mata bane kawai, maza ma na iya amfani da shi."

thesavvygirll:

"Wannan bidiyon ba zai taba tsufa ba! Akwai hikima sosai a ciki."

your_healthnp:

"Yi rayuwa don kanka. A karshe kai za ka zama a ciki kai kadai."

Fitacciyar jarumar fim ta kwanta dama

A wani labarin kuma, mun ji cewa fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finai ta kudancin Najeriya watau Nollywood, Cynthia Okereke, ta riga mu gidan gaskiya.

Abokin aikinta a masana'antar shirya fina-fanai, Joseph Okechukwu, shi ne ya sanar da labarin mutuwarta ranar Laraba (yau) 12 ga watan Yuli, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng