Bude Iyakokin Najeriya: Shugaban Kwastam Ya Yi Magana Bayan Zaman Farko Da Tinubu

Bude Iyakokin Najeriya: Shugaban Kwastam Ya Yi Magana Bayan Zaman Farko Da Tinubu

  • Shugaban Kwastam ya shaida cewa iyakoki kadan ne aka bude, akasin abin da mutane ke tunani
  • A farkon makon nan Bashir Adewale Adeniyi ya ziyarci Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Villa
  • Duk da an janye tallafin man fetur a Najeriya, CG Adeniyi ya nuna har yanzu akwai ‘yan fasa kauri

Abuja - Shugaban hukumar kwastam na kasa, Bashir Adewale Adeniyi ya yi watsi da batun da ake yi na cewa duka iyakokin Najeriya a bude su ke.

Rahoton da aka samu daga tashar Channels ya ce shugaban rikon kwaryan na NCS ya yi wannan bayani ne da yake zantawa da ‘yan jarida a Abuja.

Bayan ya yi zama da Mai girma Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban Najeriya, Adewale Adeniyi ya ce tattaunawarsu ta tabo sha’anin iyakoki.

Kara karanta wannan

Yadda APC Ta Hana Tinubu Kudi a Lokacin Kamfe In Ji Mataimakin Shugaban Jam’iyya

Iyakoki
Jami'ai a bakin iyakoki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A cewar Adewale Adeniyi, shugaban kasar ya nuna bukatar jami’an kwastam su tsare iyakoki da kyau domin samun tsaro da tabbatar da hadin-kai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Najeriya za ta hada-kai da Benin

Zuwa mako mai zuwa, shugaban kwastam din ya ce zai ziyarci kasar Benin domin ganin yadda za a hada-kai, ayi aiki tare da nufin a iya cin ma nasara.

Adeniyi ya ce Najeriya da Benin za su duba yadda za a inganta tsaro, shigo da kaya daga kasashen waje da amfani da fasaha wajen magance matsaloli.

An yi umarni a bude iyakoki?

Da aka tambaye shi ko shugaban kasa ya bada umarnin a bude duka iyakokin Najeriya, sai ya ce hakan ba gaskiya ba ne, har yanzu iyakoki na rufe.

"Sai dai zuwa yanzu wasu iyakokin ne a bude, akasin abin da mutane su ke tunani a yau.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Mai: Na San Yan Najeriya Na Shan Bakar Wahala Amma A Kara Hakuri, Tinubu Ya Fadi Tanadin Da Ya Yiwa Talakawansa

Yayin da mu ke magana, an sake bude kusan biyar daga cikinsu. Da farko an kuma bude hudu, sai kuma aka sake bude wasu iyakoki biyu.

Bayan wannan abin da ya faru, har yanzu halin da ake ciki kenan. Akwai shiri da ake yi na duba shi kan shi tasirin rufe iyakokin da aka yi."

- Bashir Adewale Adeniyi

Da ake hira da shi, Adeniyi ya koka kan yadda ake fasa-kaurin mai daga Najeriya zuwa makwabta, duk da gwamnatin tarayya ta janye tallafin fetur.

Wike da Tinubu a zaben 2023

Ba don gudumuwar kudin Gwamna Nyesom Wike a zaben 2023 ba, an rahoto Tony Okocha yana cewa da Peter Obi zai yi nasara a jihar Ribas a LP.

Cif Tony Okocha ya fadawa manema labarai cewa abin da yake taimake su a Ribas shi ne sakarcin PDP, a lokacin Nyesom Wike ya na kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng