Bayan Ayyana Sabon Farashi Da Tinubu Ya Yi, Kasuwar Masu Shigo Da Tsaffin Motoci Ta Ragu
- An samu sauye-sauye a bangaren shigo da motoci yayin da aka samu karin fiye da kashi 40 na kudin tantancewa
- Babban bankin CBN da Hukumar Kwastam a kwanakin baya sun kara kudin da kashi 40 bayan lissafin kudin haraji
- Hukumar Kwastam din har ila yau, ta kara kudin bayan lissafin kudin shigo da motar daga N422 zuwa N589 akan Dala
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja – Sabon dokar da aka kirkiro don biyan kudin tantancewa yayin shigo da motoci Najeriya ya karya masu shigo da tsaffin motocin kasar.
Karin kashi 40 na kudin tantancewar ya jawo raguwar siyan motocin yan kwatano da ake kira 'Tokunbo' da shigo da su da kashi 70.
Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar Kwastam a kwanan nan sun kara kudin da kashi 40 bayan lissafa kudin shigo da motocin, Legit.ng ta tattaro.
Yadda sabon farashin ya gurgunta masu kasuwar shigo da motocin
Punch ta tattaro cewa hukumar Kwastam din ta kara kudin bayan lissafa adadin yadda kudin shigo da mota daga N422 zuwa N589 akan Dala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Alhamis 6 ga watan Yuli, Babban Bankin Najeriya (CBN) ta kara kudin tantance motocin da kashi 31 inda aka samu bambanci daga N589 zuwa N770 akan Dala, cewar Legit.ng.
Hukumar Kwastam din ta bayyana haka ne a ranar 4 ga watan Yuli na wannan shekara wanda mataimakin kwanturola na hukumar bangaren sadarwa da ci gaba, K.I Adeola ya sanya wa hannu.
Sanarwar sauya farashin motoci daga Kwatano
A cewar sanarwar:
“CBN ta ayyana yawon farashin Naira, wanda ya kawo sauye-sauye a harkan canji na kudi, wannan doka kowa zai tabbatar da ita daga ma’aikatu da tsangayoyi da kuma sauran hukumomi har da hukumar Kwastam.”
Ta Bayyana: Tambuwal, Yari, Wammako Da Wasu Tsaffin Gwamoni 11 Da Ke Karbar Fanso Bayan Zama Sanatoci
Hukumar Kwastam ta sanarwa dukkan jami’anta na yanki su tabbatar wannan bayani ya isa inda ya dace.
Shugaban matasan kungiyar dillalan masu harkar motocin da ke ‘Tin Can Island’, Remilekun Sikiru ya ce sun samu wannan umarni a ranar Alhamis 6 ga watan Yuli.
Ya ce a baya ana tantace ‘Toyota 2014’ akan N1m amma yanzu ya kai N1.9m.
Gwamnati Ta Saki Sabon Bayani Akan Farashin Motocin Belgium a Najeriya
A wani labarin, a wani sabon rahoto an bayyana yadda motocin da aka yi amfani da su suka yi matukar faduwa da kaso 47.
Hukumar Kididdiga ta NBS ita ta fitar da wannan rahoton inda ta ce kudaden da ake siyan motocin ma ya sauko sosai.
Hukumar ta ce a shekarar 2021 yawan kudaden ya kai biliyan N617.48 yayin da ya sauko biliyan N335.05 a shekarar 2022.
Asali: Legit.ng