Kano: Kwamishina Ya Kasa-Ya Tsare, An Koma Cafke Marasa Zuwa Aiki da Wuri

Kano: Kwamishina Ya Kasa-Ya Tsare, An Koma Cafke Marasa Zuwa Aiki da Wuri

  • A safiyar yau Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya tare bakin kofar shiga ma’aikatar lafiya ta jihar Kano
  • Kwamishinan harkokin lafiyan ya yi hakan ne da nufin gano ma’aikatansa masu zuwa aiki a makare
  • Ana haka sai wani Kwamishinan, Umar Haruna Doguwa ya na cigaba da kai ziyara zuwa makarantu

Kano - Kwamishinan harkokin lafiya na jihar Kano, Abubakar Labaran Yusuf ya yi sammakon zuwa aiki domin gano marasa zuwa ofis da wuri.

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta ci karo da wasu hotuna a shafukan sada zumunta, an fahimci Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya yi ma’aikatansa a yau.

Da yake yau Litinin, sai dai aka ji Dr. Yusuf ya na zaune a wajen ofishin ma’aikatar kiwon lafiya, ya na lura da ma’aikatan da ke zuwa aiki a makare.

Kara karanta wannan

An Shiga Rudani Yayin da Jami'an Amotekun Suka Halaka Wani Mahauci Dan Jihar Sokoto a Oyo

Gwamnatin Kano
Gwamnatin Jihar Kano Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Kwamishina da gaske yake yi

Babban Mai taimakawa Gwamnan jihar Kano a kafofin sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro ya wallafa hoton dazu nan a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da wasu su ke yabawa Kwamishinan lafiyan a kan kokarin da yake yi na tabbatar da ma’aikata su na aikinsu da kyau, wasu sun buge da suka.

A cewar wasu masu bibiyar shafukan sada zumuntan zamanin, abin da Kwamishinan yake yi duk buge ne, kuma ba wannan ne aikin gabansa ba.

Hassan Ba Wasa Gama ya ce zai fi kyau Kwamishinan ya tafi zagayen asibitocin jihar Kano.

Ziyarar bazata zuwa makarantu

Ana haka sai aka samu labari daga gidan rediyon Aminci cewa Umar Haruna Doguwa wanda shi ne Kwamishinan ilmi, ya na ta ziyartar makarantu.

A wannan karo, Hon. Umar Doguwa ya kai irin ziyarar bazatan da ya saba zuwa makaranar firamare gwamnati ta Jarkasa domin ganin halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Abin da Ya Gagari Buhari, Ya Sasanta Rikicin Hukumomi 2 a Cikin Wata 1

A nan Kwamishinan ya ci karo da wasu munanan ban-dakuna da ake amfani da su a makarantar.

Daga nan kuma sai aka ji Doguwa ya shiga wata makaranta da ke unguwar Kwalli, a nan ya ba wani malami mai suna Munzali Bako kyautar N30, 000.

Wata sanarwa da aka samu ta bakin Abba Rabiu Gwarzo ta ce Kwamishinan ya yaba da kokarin wannan malami da yake fitowa yin aiki a kowace rana.

Za a binciki Abdullahi Ganduje

A wani rahoton dabam, an ji an dawo da maganar binciken tsohon Gwamna watau Abdullahi Ganduje a kan zargin karbar rashawa wajen bada kwangila.

Gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta tafi kotun tarayya, ta na neman ba Hukumar EFCC damar taso Dr. Ganduje a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng