'Ba Mu San Laifin Da Muka Aikata Ba', Wadanda Ake Zargin Yan Boko Haram Da Ke Tsare A Borno

'Ba Mu San Laifin Da Muka Aikata Ba', Wadanda Ake Zargin Yan Boko Haram Da Ke Tsare A Borno

  • Mutane da dama da ake zargin mayakan Boko Haram ne an tsare su a barikin Giwa shekara da shekaru
  • Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa ba su san dalilin da ya sa aka kama su ba ko kuma abin da suka aikata
  • Yayin wasu ke cewa sunfi shekara 10 a tsare ba tare da kai su kotu ko yanke musu hukunci ba tsawon wannan lokaci

Jihar Borno - Fiye da mutane 2000 ne da ake zargi 'yan Boko Haram ke jibge babu shari'a a barikin Giwa da ke Maiduguri cikin jihar Borno.

Wadanda aka kullen sun hada da mayakan Boko Haram da matansu da iyayensu da 'ya'yansu da sauransu.

Mutane Da Suka Hada Da Mata Da Yara Fiye Da 2,000 Aka Tsare Kan Zargin Boko
An Tsare Mata Da Yara Fiye Da 2,000 Kan Zargin Boko Haram Tsawon Shekaru. Hoto: BBC.
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa wadanda ake zargin sun dade babu shari'a saboda irin tuhume-tuhumen da ake musu daban-daban.

Kara karanta wannan

Wurare 6 Garanti Da 'Yan Mata Ka Iya Dacewa Da Samun Mazan Aure Da Suka Dade Suna Hankoro

Mutane fiye da 2,000 ne ke tsare a barikin Giwa

Wani bayani da rundunar sojin ta tabbatar, ya ce akwai mutane fiye da 2,048 tun watan Maris na wannan shekarar, wadanda suka hada da mata 35, yara maza bakwai da yara mata 10 sai manyan maza 1991.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani tsohon kwamandan 'Operation Lafiya Dole' ya bayyana cewa an samar da wurin ne don tsare masu laifi na wucin gadi, kafin yanke musu hukunci ko kuma mai da su cikin al'umma.

Yayin da wasu daga cikinsu suka ce sun fi shekara 10 a wannan wuri ba tare da kai su kotu ba ko yanke musu hukunci, inda wasu kuma suka ce sun fi shekara daya.

A nata bangaren, rundunar sojin Nigeriya ta ce wannan wuri ne da ke taimakawa wurin dakile ayyukan 'yan Boko Haram, cewar HumAngle.

Kara karanta wannan

Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo

Ya ce:

"Wannan wuri ne mai kyau da tsari ba kamar yadda mutane ke tunani ba, ba ma goyon bayan cin zarafinsu daga sojoji."

Ya kara da cewa babu wanda za a kulle a wurin na tsawon lokaci ba tare da wani hujja ba.

Mutanen sun bayyana yadda aka tsare su tsawon shekaru

A bangaren su, wadanda ake zargin mayakan Boko Haram din sun koka kan yadda suka shiga halin kunci dalilin wannan kulle.

Sun bayyana yadda tun shigarsu wannan wuri ba su sake ganin iyayensu da 'ya'yansu ba.

Mafi yawan wadanda ake tsare da su, sun ce ba su san ma dalilin da ya sa aka tsaresu ba, saboda a hanya kawai a gan su aka kama.

Sun roki gwamnati da ta dube su da idon rahama don ganin sun koma ga iyalansu.

Mutane 6 Sun Mutu A Borno Yayin Da Wani Bam Da Aka Binne Ya Tashi

A wani labarin, wani bam ya tashi tare da kashe mutane shida bayan 'yan Boko Haram sun binne shi a kan hanya.

Kara karanta wannan

"Tun Asali Abu 2 Ke Ya Kawo 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya" Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai

Lamarin ya faru ne a kan hanyar wata karkara da ke tsakanin Bama zuwa Kawuri a karamar hukumar Konduga.

Rahotanni sun ce Amir na kungiyar mayakan Boko Haram, Alhaji Ari Hajja Fusam ya ce su suka kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.