Kotu Ta Umarci Obasanjo, Yar Adu’a, Jonathan Da Buhari Su Bada Bahasin Yadda Suka Kashe $5bn Na Abacha

Kotu Ta Umarci Obasanjo, Yar Adu’a, Jonathan Da Buhari Su Bada Bahasin Yadda Suka Kashe $5bn Na Abacha

  • Wata babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci gwamnatin Tarayya ta yi bayani akan kudaden da ake zargin Abacha da badakalar su
  • Kotun ta bukaci Tinubu ya ba su bahasi kan $5bn da gwamnatoci hudu da suka shude na Obasanjo da marigayi 'Yar Adu'a, Jonathan da kuma Buhari
  • Ta kuma umarci gwamnatin ta bayyana wurare da kuma lokacin da aka yi amfani da kudaden tare da kamfanoni da 'yan kwangilar da suka yi ayyukan

FCT, Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci bayyana kasha-kashen kudade dala biliyan biyar da ake zargin tsohon shugaban kasa, Sani Abacha da karkatar da su.

Kotun ta bukaci bahasin ne da kuma yadda gwamnatoci hudu da suka wuce suka yi amfani da kudaden, gidan talabaijin na Channels ta tattaro.

Kara karanta wannan

Toh fa: Kamar Ganduje da Abba, gwamnan Arewa ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamna

Kotu Ta Umarci Obasanjo, ’Yar Adu’a, Jonathan Da Buhari Bahasin Yadda Suka Kashe Kudade Har $5Bn Na Abacha
Tsoffin Shugabannin Najeriya Tun Daga 1999. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Gwamnatoci hudun sun hada da gwamnatin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo da gwamnatin marigayi Umaru Musa ‘Yar Adu’a da Goodluck Jonathan da kuma gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Kotun ta umarci Tinubu ya ba da bahasin yadda Obasanjo, 'Yar Adu'a, Jonatahn da Buhari suka yi da kudaden Abacha

Kotun ta umarci Shugaba Tinubu da ya bayyana yawan kudin da Abacha ya yi badakalarsu da kuma yawan kudaden da aka samu yayin binciken da kuma yarjejeniyar da gwamnatoci hudun suka saka hannu a kai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkalin kotun, James Omotosho Kolawole shi ya ba da wannan umarni a makon da ya gabata bayan Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Da Tabbatar Da Gaskiya (SERAP) ta shigar da koke.

Alkalin ya umarci gwamnatin Tarayya musamman ma'aikatar kudi ta bayyana wa SERAP yadda aka kashe $5bn na Abacha cikin mako daya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: An kai karar Abba Gida-Gida Amurka, China da EU kan gallazawa Kanawa

Har ila yau, kotun ta umarci gwamnatin Tarayya ta bayyana inda aka aiwatar da ayyukan da kuma kamfanoni da 'yan kwangilar da suka aiwatar da ayyukan tun daga shekarar 1999.

Ya bukaci gwamnatin ta fadi rawar da Bankin Duniya ta taka

Alkalin ya ce dole gwamnatin Tarayya ta fadi rawar da Bankin Duniya ta taka a fannin aiwatar da ayyuka da kudaden na gwamnatoci hudu da aka lissafa.

A cewarsa:

"Ma'aikatar kudi ta bayyana cewa ba ta da kiyasin kudaden da aka sacen da kuma yadda aka yi amfani da su a ma'aikatar, inda ya ce hakan ya sabawa 'yancin sanin bayanai a kasa."

Kotun ta yi watsi da dukkan korafe-korafen gwamnatin akan haka, inda ta nuna bangaren ta na goyon bayan SERAP madadin gwamnatin Tarayya, Daily Trust ta tattaro.

Wani bangare na sanarwar hukuncin kotun

A hukuncin kotun da aka gabatar a ranar 3 ga watan Yuli, Alkalin kotun ya ce:

Kara karanta wannan

"Tun Asali Abu 2 Ke Ya Kawo 'Yan Bindiga a Arewacin Najeriya" Tsohon Gwamna Ya Fasa Ƙwai

"Rashin ba da bayanai akan yadda aka kashe kudaden ga SERAP ya sabawa 'yancin sanin bayanai.
"Ma'aikatar ba za ta ce ba ta da masaniya akan kudaden da ake zargin Abacha da sacewa ba na $5bn.
"Gwamnatin ta gagara ba da bahasin yadda aka kashe kudaden da kuma ayyukan da aka yi da su, ko kamfanoni da 'yan kwangilar da suka gudanar da ayyukan."

Za A Kasafta Kudaden Marigayi Sani Abacha Tsakanin Kasashe Uku

A wani labarin, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta kasafta kudaden marigayi Sani Abacha tsakanin kasashe uku.

Gwamnatin ta ce cikin kudaden da tsibirin Jersey ta bankado ya kai dala 267 da aka samu a wani asusu.

Gwamnatin Najeriya ta ce zata zauna da kasar Amurka don nemo hanyar da zasu raba kudin a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.