Za a kasafta kudaden marigayi Janar Sani Abacha tsakanin kasashe uku

Za a kasafta kudaden marigayi Janar Sani Abacha tsakanin kasashe uku

- Kasashe guda uku zasu kasafta kudin da aka kwato a wani asusu na kasar Jersey

- Kasashen guda uku sun hada da Najeriya, Amurka da tsibirin Jersey

Kasar Amurka da Najeriya da tsibrin Jersey sun bayyana cewa zasu raba sama da dalar Amurka 267 da tsibrin Jersey ya kwato a cikin irin kudaden da ake tunanin gwamnatin tsohon shugaban kasar mulkin soja na Najeriya, Marigayi Janar Sani Abacha ta sata ta boye a wasu bankuna na kasar.

Juma'ar da ta wuce ne dai gwamnatin kasar tsibrin Jersey ta saka dalar Amurka 267 a wani asusu data ware na musamman domin irin wadannan kudaden da suke kama dana ganima.

Wani ma'aikaci a ofishin ministan shari'a na kasar shine ya shaidawa BBC cewar har ya zuwa yanzu kasar ta Jersey ba ta gama tantance hanyoyin da zata bi domin kasafta kudin ba.

KU KARANTA: Jerin gwamnonin da suka shafe fiye da shekaru takwas akan mulki

Amma ya ce gwamnatin kasar ta ce zata zauna da kasar Amurka da Najeriya domin nemo hanyar da zasu raba kudin a junansu.

Da jimawa wata babbar kotu ta kasar Amurka ta binciko wadannan kudaden wanda ta bayyana cewa sun fito daga Najeriya daga wasu bankuna na kasar Amurka, daga baya kuma aka tura kudin zuwa bankunan tsibirin Jersey.

Ana dai zargin tsohon shugaban kasar mulkin sojan Janar Sani Abacha da dibar dukiyar kasar inda ya fitar da ita zuwa wasu kasashen waje daban-daban.

Sai dai kuma wani rahoto da muka samu ya nuna cewa kasar Birtaniya ta kwace kudaden daga wani banki na tsibirin Jersey.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel