Sweden: Sarkin Musulmi Ya Yi Allah Wadai Da Kona Qur’ani, Ya Ce Ba Za Su Lamunta Ba

Sweden: Sarkin Musulmi Ya Yi Allah Wadai Da Kona Qur’ani, Ya Ce Ba Za Su Lamunta Ba

  • Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi Allah wadai da kona Alkur’ani da aka yi a kasar Sweden a ranar babbar sallah
  • Sultan ya bayyana haka ta bakin Mataimakin Sakatare Janar na NSCIA, Farfesa Salisu Shehu a ranar Asabar 8 ga watan Yuli
  • Ya roki kasar Sweden da ta yi binciken gaggawa tare da daukar mataki don nunawa duniya cewa suna kare hakkin dan Adam

Jihar Sokoto – Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi Allah wadai da kona Alkur’ani a bakin masallacin birnin Stockholm na kasar Sweden.

Ya bayyana wannan aika-aika a matsayin cin zarafi da kuma neman tsokana wanda ya sabawa dokokin kasashe.

Sarkin Musulmin Najeriya
Sarkin Musulmin Najeriya Ya Bukaci A Yi Bincike Kan Kona Kur'ani A Sweden. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sultan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mataimakin sakatare janar na Majalisar Kula da Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Farfesa Salisu Shehu ya fitar a ranar Asabar 8 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: An kai karar Abba Gida-Gida Amurka, China da EU kan gallazawa Kanawa

Sarkin Musulmi ya bayyana takaicin yadda kasashen Turai ke cin zarafin Musulunci

Ya ce yadda kasashen Turai ke tozarta duk wasu abubuwa da suka shafi Musulunci ya nuna a fili rashin adalcinsu, cewar Premium Times.

Ya bukaci Musulmai da su kai zuciya nesa inda ya kiraye gwamnatin Sweden da su yi binciken gaggawa tare da daukar mataki.

A cewar sanarwar:

“Abin mamaki ne irin wannan sabo mai girma ta faru a kasar da ake ganin na daga cikin kasashe masu son zaman lafiya a Nahiyar Turai.
“Wannar majalisar ta kadu da jin haka a kasar inda ‘yan sandan su da ke ikirarin wayewa da sanin aiki suka gagara daukar wani mataki, inda suka ba da dama ga wani don aikata wannan kwamacala."

Ya kirayi kasar Sweden da ta dauki mataki, don ba za su lamunta ba

Sanarwar ta kara da cewa:

“Duk kasar Nahiyar Turai da ta ba da damar aikata wannan aika-aika akan Musulunci ya nuna tsagwaron rashin adalci da kimarsu, kuma sun zubar da mutuncinsu a idon duniya da kuma Musulmai da suke ikirarin sanin hakkin dan Adam musamman na addini.”

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Zargi Muhammadu Buhari, Sanatoci Za Su Binciki Tsohuwar Gwamnati

Majalisar ta kirayi kasar Sweden da ta yi gaggawar bincike da kuma daukar matakin da ya dace da kuma bayyana wa duniya sakamakon binciken don tabbatar da adalci, Tribune ta tattaro.

Majalisar har ila yau, ta roki al’ummar Musulmi da su kai zuciya nesa don samun zaman lafiya da kuma zama masu bin doka don gudun daukar doka a hannu, cewar Punch.

Limaman Coci A Arewacin Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Kona Alkur'ani A Sweden

A wani labarin, limaman majami'a a Arewacin Najeriya sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani a Sweden.

Gamayyar limaman sun yi kira da Musulimi da su kai zuciya nesa yayin da suka ce a shirye suke su kare martabar Alkur'ani.

Rabaran Dakta Noble James da Fasto Yohanna Buru sun bayyana kaduwarsu yadda gwamnatin kasar ta bar hakan ta faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.