Babbar Magana Yayin da Wata Kungiya Ta Kai Kuka Amurka, EU da China, Ta Bukaci Hana Abba Gida-Gida Biza
- Wata kungiyar farar hula na neman a sanya wa Abba Kabir Yusuf, gwamnan Kano takunkumi a kasashen waje
- CGGCI ta nemi a hana Abba da ahalinsa shiga wasu kasashe saboda gallazawa Kanawa da ya yi da rusau
- Gwamnan na ci gaba da bayyana gaskiyarsa da kuma aniyarsa ta dawo da kadarori da filayen gwamnati da aka siyar a jihar
FCT, Abuja - Kungiyar hadin gwiwar gangamin shugabanci nagari da sauyi ta CGGCI ta kai karar gwamnatin Abba Gida-Gida ga Amurka, Tarayyar Turai, China da sauran kasashe kan rusa gine-gine da yake a Kano, Vanguard ta ruwaito.
Gamayyar, a cikin wata takardar koke dauke da sa hannun kodinetanta na kasa, Kwamared Okpokwu Ogenyi, ta bukaci a haramtawa gwamnan da iyalansa biza saboda gallazawa Kanawa.
Dalilin da yasa kungiyar ta damu
Kungiyar ta bayyana damuwar cewa, aikin da Abba Kabir Yusuf ya fara a makon farko na mulkinsa ya saba da tafarkin dimokaradiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, ta ce hakan take hakkin dan Adam ne, kana ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi, wanda kuma hakan damuwa ne gareta.
A cewar gamayyar:
“Ayyukansa sun saba da tsarin dimokradiyya kana take hakkin dan adam ne.”
Sako ya isa ga ofisoshin da suka dace
Tuni dai wasikar ta isa ga wadanda suka dace a ofisoshin jakadancin kasashen da kuma na tarayyar turai a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuli, 2023, Leadership ta ruwaito.
A cewar kwafin takardar da aka rabawa manema labarai a ranar Asabar, kungiyar ta ce a yayin rusau din na Kano, an yi asarar rayuka wanda ke da matukar tasiri ga zaman lafiya kuma ya zama damuwa ga kungiyar.
Wata Kungiya Ta Nemi a Gudanar Da Bincike Na Gaggawa Kan Yadda Gwamnan Zamfara Dauda Lawal Ya Tara Dukiyarsa
Ya zuwa yanzu, Abba Kabir Yusuf na ci gaba da bayyana dalilai da kuma kare kansa daga wannan rusau da yake a Kano.
Ko gezau: Abba Gida-Gida ya ce rusau ba ja da baya
A wani labarin, kunji yadda gwamnan Kano ya bayyana cewa, bai yi dana-sanin yin rusau din yake ci gaba da yi a jihar ba.
Ya ce yana yin hakan ne domin kwato kadarori da filayen gwamnatin da aka kwace ba gaira babu dalili.
Ya kuma bayyana cewa, ba zai rintsa ba har sai ya tabbatar da kwato duk wani filin da gwamnatin baya ta siyarwa jama’a.
Asali: Legit.ng