“Musulunci Ba Zai Baki Kunya Ba”: Mijin Jaruma Mercy Ya Jinjina Mata Yayin da Suka Kammala Aikin Hajji

“Musulunci Ba Zai Baki Kunya Ba”: Mijin Jaruma Mercy Ya Jinjina Mata Yayin da Suka Kammala Aikin Hajji

  • Mercy Aigbe da mijinta Adekaz suna cikin miliyoyin al'ummar Musulmi da suka yi aikin hajji a bana
  • Da kammala aikin hajjinsu, dan kasuwar ya wallafa sakon jinjina ga matar tasa sannan ya yi mata maraba da shiga addinin Musulunci a hukumance
  • Adekaz ya kuma wallafa bidiyon matarsa tana yi masa addu'a da godiya ga Allah da ya yi amfani da shi wajen kai ta kasa mai tsarki

Jarumar Nollywood Mercy Aigbe ta yi godiya ga Allah madaukakin sarki da ya yi amfani da mijinta wajen kai ta aikin hajji a kasa mai tsarki.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram, mijin jarumar mai suna Adekaz ya wallafa wani bidiyo inda jarumar ke nuna godiyarta ga Allah da ya yi amfani da shi wajen kai ta garin Makkah domin sauke farali.

Kara karanta wannan

“Wa Ya Shirya Aurena”: Baturiya Ta Yi Alkawarin Bayar Da Kyautar Biza Ga Duk Mutumin Da Ya Shirya Aurenta

Jaruma Mercy da mijinta a Saudiyya
“Musulunci Ba Zai Baki Kunya Ba”: Mijin Jaruma Mercy Ya Jinjina Mata Yayin da Suka Kammala Aikin Hajji Hoto: @kazimadeoti
Asali: Instagram

Mercy wacce ke tattare da alamun gajiya ta kuma yi wa mijin nata ruwan addu'o'i, tana mai rokon Allah ya azurta shi.

Adekaz ya rubuta dadadan zantuka a jikin bidiyon yana mai yabawa matarsa da tabbatar da yadda yake alfahari da ita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma yi mata maraba da shigowa Addinin Musulunci sannan ya ba ta tabbacin cewa Musulunci ba zai taba bata kunya ba.

"Alhamdulilai robil al-amin . Godiya ga Allah da muka kammala aikin Umrah/Hajjinmu na 2023. Ina mai farin ciki da ke, Alhaja Minnah kuma na san cewa Allah na farin ciki da ke. Ina iya yi maki alkawarin cewa addinin Musulunci ba zai taba baki kunya ba, Amin. Allah ya amsa ibadu da addu'o'inmu. Kuma ga duk wanda ke burin zuwa kasa mai tsarki a Saudiyya, Allah ya cika masa burinsa sannan ya saukaka maku. Amin. Jummah Mubarak ☪️"

Kara karanta wannan

“Sharadi Ba Za Ka Yi Mun Kishiya Ba”: Budurwa Ta Yi Alkawarin Baiwa Duk Wanda Ya Aureta Gida, Mota da Miliyan 50 a Bidiyo

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

amopeakewi:

"Mosha Allah na gaza rike hawayena Allah ya ci gaba da yi wa gidanki albarka Alhaja Minna, Allah ya kara arziki dadi."

thelordismyshephard:

"Ina yi maki fatan alkhairi Hajiya. Rahamaar Allah a kodayaushe."

semaiib:

"Ganin cewa bata sanya hakorin makkah ba walahi i ina kaunarki sosai.... Monsha Allah ga dukkan addu'o'inki ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️"

oladoja_rukayat:

"Masha Allah ❤️❤️❤️❤️ Allah madaukakin sarki ya karba a matsayin ibadah "

Jarumar fim Mercy ta burge masoya bayan ta saki zafafan hotunansu da mijinta a Saudiyya

A wani labarin kuma, Mercy Aigbe na daya daga cikin yan tsirarun jarumai da suke sauke farali a garin Makkah, kuma tana ta baiwa masoyanta karin bayani kan yadda abubuwa ke gudana.

Jarumar ta yi sabon wallafa a shafinta, tana mai nunawa duniya mijinta a hotuna daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng