Tsohon Gwamna Ya Rubuta Wasika, Ya Nemi a Daina Biyan Shi Fanshon N670, 000 a Wata
- Gbenga Daniel ba zai hada fanshon tsohon Gwamna da albashin majalisar dattawa a lokaci daya ba
- Tsohon Gwamnan ya bukaci Gwamnatin Ogun ta tsaida fansho da alawus dinsa tun da ya zama Sanata
- Sanata Daniel ya yi Gwamna a jihar tsakanin 2003 da 2011, saboda haka ana biyansa a kowane wata
Abuja - Gbenga Daniel bai bukatar gwamnatin Ogun ta rika biyan shi fansho da duk wani alawus da ya cancanta saboda zamansa tsohon Gwamna.
A dandalin Twitter, Sanata Gbenga Daniel ya sanar da cewa tuni ya rubutawa gwamnatin jihar Ogun wasika cewa a dakatar da biyansa fansho.
Tsohon Gwamnan ya na cikin wadanda su ka lashe zaben majalisar dattawa da aka yi a farkon shekarar nan, yanzu Sanata ne a inuwar jam’iyyar APC.
Albashi 2 a lokaci 1
Ganin zai rika karbar albashi biyu lokaci guda, Sanata Daniel ya rubuta wasika zuwa ga Gwamna Dapo Abiodun cewa a tsaida fansho da alawus dinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘Dan siyasar yake cewa hankalinsa ba zai kwanta idan ya lakume wadannan kudi shi kadai ba. A Najeriya, yin hakan bai ci karo da wata doka ba.
Maganar da Daniel ya yi a shafinsa
"Bayan an rantsar da ni a majalisar dattawa, na rubutawa Mai girma Prince Dapo Abiodun MFR, CON wasika a ranar 14 ga watan Yuli 2023
Na sanar da shi matakin da na dauka cewa a dakatar da biya na N676,376.95k a matsayin fansho da albashi na tsawon Gwamna a jihar Ogun.
The Cable ta ce wasikar ta nuna Sanatan bai taba amfana da wasu kudi na dabam bayan fanshon ba.
Daga lokacin da ya bar kujerar Gwamna a 2011, Daniel ya ce bai mori kudin asibiti, zirga-zirga ko na sayen kayan daki daga hannun gwamnati ba.
A wasikar da ya aikawa Gwamna mai-ci, sabon Sanatan ya ce matakin nan da ya dauka na hakura da cin fansho a yanzu ya fi zama kusa da daidai.
Binciken Bidiyon Dala a Kano
A Kano kuwa, rahoton da mu ka samu shi ne an dawo da maganar binciken fai-fen rashawar Daloli a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin jihar Kano ta na neman ba Hukumar EFCC damar taso Abdullahi Ganduje a gaba. Hakan na faruwa ne bayan an yi canjin Gwamnati.
Asali: Legit.ng