Kano: PCACC Ta Fadi Matakin Da Za Ta Dauka Idan Ganduje Bai Amsa Gayyatarta Ba
- Shugaban Yaki da Cin Hanci a Kano, Muhuyi Magaji Rimingado ya bayyana matakin da za su dauka idan Ganduje bai amsa gayyatarsu ba
- Muhuyi ya fadi haka ne yayin hira da ‘yan jaridu a yau Alhamis 6 ga watan Yuli inda ya ce sun rubuta wasikar gayyatar Ganduje a mako mai zuwa
- Ya ce doka ta na da karfin iko, amma za su tabbatar sun ba wa tsohon gwamnan daman kare kansa tun da bai amince da zarginsa da ake yi ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano – Hukumar Sauraran Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci a Kano (PCACC) ta bayyana matakin da za ta dauka idan tsohon gwamna Ganduje ya ki amsa gayyatarta.
Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimingado shi ya bayyana haka yayin hirarsa da 'yan jaridu a yau Alhamis 6 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan
Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

Source: Facebook
Ya ce hukumar ta rubuta wasika zuwa ga tsohon gwamnan da ya bayyana a gabanta a mako mai kamawa don amsa wasu tambayoyi.
Ya bayyana matakin da za su dauka idan Ganduje ya ki amsa gayyatarsu
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Na saka hannu a wasikar da muka gayyace shi don wasu tambayoyi a mako mai zuwa saboda haka dokar kasa ta ce kuma za mu ba shi dama ya kare kansa."
Da aka tambayi Muhuyi wani mataki hukumar za ta dauka idan Ganduje bai amsa wannar gayyatar ba, sai ya ce:
“Akwai abin da doka ta tanadar, doka ta na da karfi, ta na saka biyayya ‘yar dole. Doka ba ta rokon mutum ya zo ya yi wani abu, akwai ka’idoji kuma zamu bi duk hanyar da ta dace don yin abin da ya dace.”

Kara karanta wannan
Dakyar na sha: Da jini na ya hau idan na fadi zaben sanata, tsohon shugaban APC ya magantu
Hukumar ta ce za ta ba wa Ganduje daman wanke kansa akan zargin
Ya ce binciken zai ba wa tsohon gwamnan daman wanke kansa akan zarge-zargen da ake masa, tun da ya wanke kansa a kafafen yada labarai, Channels TV ta tattaro.
Daily Trust ta tattaro cewa an wallafa bidiyon tsohon gwamnan ya na dura daloli a aljihunsa, wanda hukumar ta sanar da sabon bincike akan badakalar.
Kotu Ta Umarci Tsare Tsohon Kwamishinan A Kano Har Kwanaki 12 Kan Zargin Handame N1bn
A wani labarin, kotun da ke zamanta a jihar Kano ta umarci ci gaba da tsare tsohon kwamishinan Ganduje har kwanaki 12.
Kotun ta ce wannan umarni zai ba wa hukumar yaki da cin hanci a jihar daman samun lokacin kara bincike.
An kama tsohon kwamishinan, Idris Wada da wasu daraktoci guda uku da kuma sakataren din-din-din kan badakalar N1bn.
Asali: Legit.ng