Fashin Fadar Sarkin Minna: Binciken Yan Sanda Ya Nuna Akwai Hannun Dan Cikin Gida
- Dogarawan da aka harba yayin fashin da aka kai fadar sarkin Minna a ranar Talata, sun mutu
- Rundunar yan sanda ta ce binciken farko da aka gudanar ya nuna da dan cikin gida aka hada kai wajen kai farmakin
- Maharan sun yi awon gaba da kudi naira miliyan 3.3 yayin harin kamar yadda kwamishinan yan sandan jihar ya sanar
Niger - Rahotanni sun kawo cewa dogarawa biyu da aka harba yayin da yan fashi shuka farmaki fadar sarkin Minna a ranar Talata, 4 ga watan Yuli, sun kwanta dama.
Wani ganau ya sanar da jaridar Daily Trust cewa dogarawan na samun kulawar likitoci a babban asibitin Minna.
Yayin da yake martani a kan lamarin, da ya bayyana a matsayin abun kaduwa, Gwamna Mohammed Bago ya yi wa dogarawan fatan samun lafiya.
Sai dai kuma, da yake jawabi ga manema labarai a gefen taron kwamitin jihohin G-7 a Abuja a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, kwamishinan yan sandan jihar Neja, Mista Ogundele Ayodeji, ya ce dogarawan sun mutu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bincike ya gano an hada kai da dan cikin gida, Kwamishinan yan sanda
Ya kara da cewar binciken farko da aka gudanar ya gano an hada kai da wani dan cikin gida, yana mai cewa yan fashin sun yi awon gaba da naira miliyan 3.3.
Kwamishinan ya bayyana cewa tuni jami'ansa suka fara bibiyar masu laifin, sannan ya nuna yakinin cewa za a kama su.
Jaridar Daily Trust ta nakalto Ayodeji yana cewa:
"An kira ni da misalin karfe 3:00 na yamma yayin da nake Abuja don taron kwamitin jihohin G-7, cewa an kai harin fashi da makami a gaban fadar sarkin Minna.
"Daga bayan da na samu, bata garin sun bi sahun kashiyan masarautar har zuwa gaban kofar fadar. Yayin da kashiyan ke gab da shiga fadar, sai miyagun suka fara harbi kan mai uwa da wahabi, sannan cikin haka suka kashe dogarawan fadar biyu tare da awon gaba da miliyan 3.3.
"Daga rahotannin da na samu, akwai alamun an hada kai da wani dan cikin gida wajen aikata laifin, kuma ina da karfin gwiwar cewa za a kama masu laifin ko bajima ko badade."
Ya bayyana dandamalin G-7, wanda suka hada da babban birnin tarayya da jihohi shida da ke makwabtaka a matsayin dabara na musamman domin yakar laifukan iyakoki a tsakanin jihohin.
Ya bayyana cewa kwamitin G-7 sun hada da shugabannin tsaro na FCT, Benue, Kaduna, Kogi, Nasarawa, Neja da Filato.
'Yan Fashi Sun Kai Farmaki Fadar Mai Martaba Sarkin Minna, Sun Harbi Mutum 2
A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu 'yan fashi ɗauke da bindigu sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, da yammacin ranar Talatan nan da muke ciki.
Yan fashi da makamin sun kutsa kai fadar kuma sun harbi dogarai biyu a harin wanda ake tsammanin sun biyo ɗaya daga cikin hadiman fadar ne tun da farko.
Asali: Legit.ng