Tsofaffin Janarori Sun Jero Shawarwarin Da Za Su Kawo Karshen Matsalolin Tsaro

Tsofaffin Janarori Sun Jero Shawarwarin Da Za Su Kawo Karshen Matsalolin Tsaro

  • Wasu da su ka yi aikin damara sun kawo shawarar yadda za a magance rashin tsaro a kasar nan
  • Tsofaffin sojoji sun yi kira ga hafsun tsaron da aka zaba da su dauki darasi daga magabatansu
  • An yabi Bola Tinubu a kan zabinsa, an yi kira da a kyale shugabannin tsaron su yi aikin da ya dace

Abuja - A makon nan ne wasu gogaggu a kan harkar tsaro a Najeriya, su ka kawo shawarar yadda za a bi domin inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Punch ta ce tsofaffin sojojin nan sun bada shawara cewa sababbin hafsoshin da su ka karbi ragamar tsaro su yi koyi da magabatansu domin su iya daukar darasi.

Birgediya Janar Bashir Adewinibi mai ritaya yake cewa akwai bukatar shugabannin sojoji da harkokin tsaro su duba nasarori da kura-kuran da aka yi a baya.

Kara karanta wannan

Tsaro: Bukarti Ya Barranta Da Yerima, Ya Bayyana Matakin Da Ya Kamata A Dauka Akan 'Yan Bindiga

Tinubu da Sojoji
Bola Ahmed Tinubu (GCFR) da Nuhu Ribadu (NSA) da hafsoshin tsaro Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Janar Adewinibi ya ce zai kyau hafoshin su yi nazarin abubuwan da su ka faru kafin shigansu ofis, sai su gyara kura-kuran da aka yi a shekarun da su ka wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar tsohon sojan, hafsun sojojin da su ka sauka sun yi kokari wajen dakile ta’addanci da sauran laifuffuka, amma ba za a rasa bangarori da aka gaza ba.

"Akwai bukatar a hada kai"

Jaridar ta rahoto Birgediya Janar Peter Aro (retd.) ya na yin kira ga hafsoshin tsaron da aka nada da su hada-kansu, su yi aiki tare domin su iya cin ma nasara.

Janar Aro mai ritaya ya ce kyau a kyale shugabannin tsaro su yi aiki ba tare da katsalandan ba.

A cewar Janar Aro, Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo wajen nada wadanda su ka dace, ya ce shugaban Najeriyan ya zakulo jam’an da sun san dawar garin.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fuskanci Barazana, Lauyoyi 8 Za Su Kai Shi Kotu Kan Harajin Abin Hawa

Shawarar Janar Atolagbe Da CP Ojukwu

Abin da zai taimaka shi ne hafsoshin sojojin sama, kasa da na ruwa ‘yan aji daya ne a gidan soja, wannan zai sa su ji dadin wajen ba ‘yan sanda gudumuwa.

Manjo Janar Anthony Atolagbe ya na ganin idan ana so a fita daga halin ha’ula’i, sai hafsoshin sun rika sauraron ra’ayi da shawarar kananan jami’an sojoji.

Emmanuel Ojukwu wanda ya yi ritaya a matsayin Kwamishinan ‘yan sanda ya ce al’umma su na fatan sababbin shugabannin za su dage su inganta tsaro.

Hafsun sojoji sun je Aso Rock

A yammacin Litinin aka ji labari Nuhu Ribadu da hafsun tsaro sun yi zama da Mai girma Bola Tinubu a fadar Aso Villa, har ya ce tsaro ya karu a yanzu.

Game da dalilin zuwansu fadar shugaban Najeriya, mai bada shawara kan harkokin tsaro ya ce sun samu lokaci ne su godiya a kan mukamin da aka ba su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng