Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf Ya Soke Karin Girman Da Ganduje Ya Yi Wa Malaman Makaranta a Jihar
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida, ya soke karin girman da gwamnatin Ganduje ta yi wa wasu malaman makaranta a jihar
- Hakan na zuwa ne bayan da wasu daga cikin malaman da abin ya shafa, suka fara sauya tsarin rayuwarsu zuwa sabon karin albashin da suka samu
- Malaman sun yi kira ga gwamnan da ya dubi halin da suka tsinci kansu a ciki sakamakon matakin da ya dauka
Kano - Gwamnatin Abba Gida Gida, ta soke karin girman da tsohuwar gwamnati ta Abdullahi Ganduje ta yi wa malaman makaranta.
Gabanin saukarsa daga kan karagar mulki, Ganduje ya karawa wasu malaman firamare da na kananun sakandiren girma.
Baya ga karin girma, an kuma karawa malaman albashi a watan Afrilu da Mayu, inda aka soke karin albashin a watan Yuni.
Malaman sun ce matakin ya shafi kasafin da suka yi na babbar sallah
Wasu malaman da suka zanta da Premium Times, sun ce ba su yi tsammanin gwamnati za ta dauki irin wannan matakin ba. Wasu kuma sun ce hukuncin ya shafi lissafin da suka tsarawa kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani daga cikin malaman ya bayyana cewa an masa karin albashi sau biyu ne, a shekarar 2017 da kuma 2023, inda ya samu karin kudi N14,000. Sai dai ya ce a watan Yuni an biya shi albashi ba tare da karin da aka yi masa ba.
Wani daga cikin malaman ya bayyana cewa:
"Albashina ya koma yadda ake biya na can baya kafin karin girman, wannan ya biyo bayan kasafin kudin bikin Sallah da na riga da na yi."
Wani malamin karamar sakandire a karamar hukumar Fagge, ya ce ya samu karin girma daga mataki na 9 zuwa na 13 bayan shafe shekaru goma yana jiran a yi masa karin girman.
Malamin ya ce sabon albashinsa na N74,000 an mayar da shi tsohon albashinsa N44,000.
A cewarsa:
“Abin ya zo min da matukar mamaki, ko kadan ban taba tsammanin cewa za a soke karin girman da gwamnati ta yi min bayan ya tabbta ba, na yi imanin cewa wannan shi ne karo na farko da irin haka ta taba faruwa a tarihin Najeriya.”
Malaman sun roki gwamnatin Abba Gida Gida da ta duba halin da suke ciki
Malaman sun zargi gwamnan da rashin kula da halin da suke ciki, inda suka kara da cewa matakin da gwamnatin ta dauka na janye karin karin girma da aka yi musu bayan tsawon lokaci, ya kawo musu cikas lokacin bikin babbar sallah.
Shugaban kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) reshen jihar Kano, Baffa Ibrahim, ya ce malaman da ke karkashin ilimin bai daya na jihar ne gwamnatin ta janyewa karin girman da aka yi musu.
Malam Ibrahim ya ce kungiyar na rokon gwamnati da ta sake duba matakin da ta dauka domin walwalar malaman.
Jaridar Leadership a makon da ya gabata, ta kawo rahoton Ganduje da ya yi Allah wadai da dakatar da albashin ma'aikata 10,000 da gwamnatin Abba Gida Gida ta yi.
Kwankwaso ya musanta zargin juya Abba Gida Gida
Legit.ng ta kawo muku rahoto a baya wanda jagoran jam'iyyar NNPP, kuma shugaban darikar Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yana musanta zargin da ake masa na cewa shi ke juya gwamnatin Abba Gida Gida.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na gidan rediyon Faransa a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng