Gwamnatin Sweden Ta Yi Allah Wadai Da Kona Kur'ani, Ta Ce Babu Yawunta A Ciki

Gwamnatin Sweden Ta Yi Allah Wadai Da Kona Kur'ani, Ta Ce Babu Yawunta A Ciki

  • Gwamnatin kasar Sweden ta yi Allah wadai da kona Alkur'ani mai girma a kasar, ta ce babu yawunta a ciki
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar inda ta ce hakan ya sabawa dokokin kasar
  • Ta ce babu muhallin wariyar addini ko na launin fata da kabilanci a kasar, inda ta ce kone duk wani littafi mai tsarki laifi ne

Tun bayan kona Alkur'ani mai girma a kasar Sweden kasashe da dama musamman na Musulmi ke Allah wadai da wannan aika-aika.

Ana zargin gwamnatin kasar da goyon bayan wannan danyen aikin, inda rahotanni suka tabbatar cewa hakan ya samu goyon bayan 'yan sanda da wata kotu.

Gwamnatin Sweden ta yi Allah wadai da kona Alkur'ani a kasar
Aika-aika A Kasar Sweden Ya Jawo Tashin Hankali A Duniya. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Amma a wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar, ta ce ba ta tare da wannan aika-aika kuma ta yi Allah wadai da hakan, Aminiya ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Ta Sha Alwashin Kakaba Wa Dalibai Harshen China A Jami'o'i, Ta Roki Alfarma

Sweden ta yi Allah wadai da kona Alkur'ani

Sanarwar daga ma'aikatar harkokin wajen kasar ta musanta cewa da yawunta aka yi, inda suka nuna kyamar wannan danyen aiki na nuna kin jinin Musulunci, cewar Vanguard.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar sanarwar:

"Gwamnatin Sweden ta lura da yadda aka nuna kin jinin Musulunci a fili lokacin yin zanga-zangar, kuma ta na Allah wadai da hakan.
"Wannan lamari ya sabawa ra'ayin gwamnatin kasar, kuma ta na Allah wadai da kakkausar murya.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Kone duk wani littafi mai tsarki babban laifi ne a kasar, kuma yunkuri ne na tunzurawa da fusata mutane da kuma rashin da'a.

Ta ce wariyar addini ko launin fata babu muhallinsu a kasar

Nuna wariya musamman na addini ba shi da wurin zama a kasar nan, ko kuma wariyar kabilanci da na launin fata."

Kara karanta wannan

Cikin Fushi, Fafaroma Francis Ya Yi Martani Kan Kona Kur’ani Da Wasu Mutane Suka Yi a Sweden

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a ranar Laraba ne 28 ga watan Yuli wanda ya kasance ranar babban sallah wani matashi ya kona Alkur'ani a bakin masallacin Juma'a a birnin Stockholm.

Inda Kungiyar Kasashen Musulmi (OIC) ta yi Allah wadai da kuma daukar matakin bai daya don karewa da kuma dakile faruwar hakan a gaba.

Sweden: OIC Ta Bayyana Matakan Da Za Ta Dauka Don Kare Martabar Alkur'ani

A wani labarin, Kungiyar Kasashen Musulmi (OIC) ta yi Allah wadai da kona Alkur'ani mai girma a kasar Sweden.

Kungiyar ta ce dole a dauki matakin bai daya don karewa da dakile faruwar hakan a gaba.

Kasashe da dama sun yi Allah wadai da wannan aika-aika musamman kasashen Larabawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.