Yariman Bakura Ya Gana Da Shugaba Tinubu, Ya Ba Shi Shawarar Yin Sulhu Da 'Yan Bindiga

Yariman Bakura Ya Gana Da Shugaba Tinubu, Ya Ba Shi Shawarar Yin Sulhu Da 'Yan Bindiga

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura ya shawarci Shugaba Tinubu ya yi sulhu da ƴan bindiga
  • Tsohon gwamnan ya nuna hikima da alfanun da hakan zai samar wajen magance matsalar tsaron da ake fama da ita
  • Yariman Bakura ya yi nuni da cewa a baya an tattauna da tsagerun Niger Delta har aka yi musu afuwa, su ma ƴan bindigan sun cancanci haka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yariman Bakura, ya yi kiran da Shugaba Bola Tinubu, ya yi sulhu da ƴan bindigan da suka addabi mutanen yankin Arewa maso Yamma.

Jaridar Premium Times ta ce Sani Yarima ya bayyana hakan ne lokacin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya sanya labule da Shugaba Tinubu ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Dakyar na sha: Da jini na ya hau idan na fadi zaben sanata, tsohon shugaban APC ya magantu

Yarima ya shawarci Tinubu ya yi sulhu da 'yan bindiga
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura Hoto: Pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Yarima ya ce yakamata a tattauna da ƴan bindiga

Ya bayyana cewa yakamata wannan gwamnatin ta kawo sulhu irin wanda ya samar da shirin afuwa ga tsagerun yankin Niger Delta bayan sun tattauna da gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar'adua, cewar rahoton Vanguard.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Mutanen nan ƴan Najeriya ne sannan na yi amanna cewa sojojin ƙasar nan suna da kayan aikin da za su iya ƙarar da su idan aka basu umarni da isassun kayan aikin da su ke buƙata, da duk wani taimako."
"Amma asarar da za a yi idan aka bi wannan hanyar shi ne na yi amanna cewa yakamata a kaucewa. A baya, marigayi Shugaban ƙasa Umaru Yar'adua ya yi sulhu da tsagerun Niger Delta kuma an yi nasara."
"An kama ƴan bindiga da yawa da halaka su, ba wai ina cewa gwamnati ta ci gaba da yin sulhu da su bane har sai baba ta gani, aa abinda na ke nufi shi ne a kira su a zauna da su."

Kara karanta wannan

Yariman Bakura Ya Shawarci Gwamnatin Tinubu Ta Yi Sulhu Da Yan Bindiga

"Waɗannan mutanen waɗanda su ke tuba a kowane addini, musulunci, kiristanci, da sanin cewa Allah da ya haliccce mu yana yin yafiya idan mutum ya tuba. Saboda haka ban ga dalilin da zai sanya ace wai ƴan Najeriya ba za a yafe musu ba idan sun tuba."
"Idan sun tuba sai a sauya musu tunani su dawo cikakkun mutane sannan a dawo da su cikin al'umma, daga nan sai a ɗauki matakan kare sake aukuwar wannan bala'in.

Sulhu Na Gaskiya Yakamata Ayi Da 'Yan Bindiga

Ko a baya rahoto ya zo kan yadda Ahmed Sani Yariman Bakura ya yi kiran da ayi sulhu na gaskiya da ƴan bindigan da suka addabi mutane a jihar Zamfara da sauransu.

Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya ce sulhun na gaskiya da ƴan bindiga zai yi tasiri wajen magance matsalar tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Matsaya Kan Cire Tallafin Mai da Wasu Tsarukan Shugaba Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel