Miyetti Allah Ta Koka Kan Kama Fulani Da Akeyi a Anambra Ba Tare Da Sun Aikata Laifi Ba
- Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen Kudu maso Gabas, Alhaji Gidado Siddiki, ya koka kan yadda ake takurawa Fulani makiyaya a yankin
- Ya bayyana cewa ana kama Fulani makiyaya a garkame su a gidajen yari ba tare da sun aikata wani laifi ba
- Siddiki ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi kokarin kawo karshen muzgunawar da ake yi wa fulani a yankin
Awka, jihar Anambra - Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta makiyaya masu kiwon dabbobi (MACBAN), reshen shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya, Alhaji Gidado Siddikki, ya yi ikirarin cewa ana tsare da mambobin kungiyar a gidajen yari ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba a jihar Anambra.
Siddikki ya kuma yi zargin cewa an yi wa wasu daga cikin Fulani makiyaya sharri da cewa suna garkuwa da mutane da fashi da makami inda jami'an 'yan sanda ke tsare su sama da shekaru biyar ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.
Kone Al-Qur'ani a Sweden: Kungiyar Musulmai Ta Fadi Matakan Da Za Ta Dauka Don Kare Martabar Alkur'ani A Fadin Duniya
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Awka, babban birnin jihar ta Anambra a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Shugaban MACBAN ya roki gwamnatin jihar ta magance muzgunawar da akewa Fulani
Ya roki gwamnatin jihar Anambra ta hannun ma’aikatar shari’a da hukumar gidajen yarin jihar da ta duba lamarin, da nufin kawo karshen matsalar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Shugabancin MACBAN a wannan shiyya ba ya jin dadn yadda ake wulakanta Fulani makiyaya da kuma lakaba masu laifin garkuwa da mutane da fashi da makami a yankin."
“Mun zo nan ne domin gudanar kasuwancinmu, wanda dukkanmu muna sane da cewa kiwon shanu ne da ake killacewa a jeji ba wai don aikata laifuka ba."
“Akwai da yawa daga cikin mutanenmu da suka kwashe sama da shekaru biyar a gidan yari ba tare da gwamnatin jihar ta duba fayil dinsu ba ko kuma ta yi musu shari’a."
"Duk da dai wannan ƙiyayya ta samo asali ne daga wasu mutane da ke zaune tare da 'yan kabilar Igbo waɗanda ba sa son Fulani a yankin."
“Duk inda suka ga Bafulatani saboda tsana, sai su kai shi ofishin ’yan sanda mafi kusa, sannan su lakaba masa wani babban zargi, ko ya aikata laifin ko bai aikata ba, ‘yan sanda za su kama shi, su gurfanar da shi a gaban kotu, daga nan sai a jefa gidan yari kuma a ajiye fayil dinsa gefe guda ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba."
“Don haka, a madadin kungiyar MACBAN ta Kudu maso Gabas, ina kira ga gwamnatin jihar Anambra, ta hannun ma’aikatar shari’a da hukumar gidan yari da ke jihar, da su duba lamarin, domin mutanenmu da ke tsare a gidan yari su samu 'yanci ko kuma a yanke masa hukumci kamar yadda dokar Tarayyar Najeriya ta tanada."
MACBAN ta goyi bayan a hukunta duk wanda aka samu da aikata laifi
Siddiki ya kuma ba da tabbacin cewa, kungiyar na goyon bayan hukunta duk wani Bafulatani da aka kama da laifin aikata wani laifi a yayin gudanar kiwo.
Nigerian Tribune ta ruwaito kungiyar na bayyana cewa ta aminta da a hukunta ko waye aka samu da laifi kamar yadda dokar kungiyar ta tanada.
Ya kuma jaddada cewa kungiyar MACBAN shiyyar Kudu maso Gabas, a karkashin ikonsa za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin yankin.
Kungiyar Fulani ta nemi a sanya mutanenta cikin mukaman gwamnatin Tinubu
Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wata kungiya ta Fulani masu kiwon dabbobi ta Najeriya (KACRAN), da ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya tafi da mambobin kungiyar a gwamnatinsa.
Kungiyar ta koka kan irin yadda ake kin sanya Fulani a cikin sha'anin gwamnati a Najeriya.
Asali: Legit.ng