Dangote Ya Bayyana Cewa Ba Shi Da Gida Ko Daya A Kasashen Waje, Amma Ma'aikatansa Suna Da Shi

Dangote Ya Bayyana Cewa Ba Shi Da Gida Ko Daya A Kasashen Waje, Amma Ma'aikatansa Suna Da Shi

  • Mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ba shi da gida ko guda ɗaya a ƙasar waje
  • Hamshaƙin ɗan kasuwar ya ce yasan wasu daga cikin ma'aikatansa da ke da gida a ƙasar Birtaniya
  • Dangote ya shawarci 'yan kasuwa masu tasowa da su guji biyewa ƙylale-ƙyalen duniya, don gudun kar ya ɗauke musu hankali daga kasuwancinsu

Alhaji Aliko Dangote, attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afrika ya bayyana dalilin da ya sa bai mallaki gida ko guda ɗaya ba a ƙasashen waje.

Dangote ya bayyana cewa duk da cewa wasu daga cikin ma'aikatan da ke aiki a ƙarƙashinsa suna da gidajen da suke zuwa hutu a waje, ya zaɓi ya zauna ba tare da mallakar gida a ƙasar waje ba.

Kara karanta wannan

"Ba Haka Aka So Ba": Tabo Ya Bata Kwalliyar Amarya a Ranar Biki, Hotunan Sun Yadu

Dangoten ya yi bayanin ne a wata hira da ya yi da Business Insider Africa, wacce aka wallafa a shafin Instagram na Tony Elumelu foundation.

Ba na da gida ko guda daya a kasar waje - Dangote
Dangote a ce bai da gida ko guda daya a kasar waje. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Dangote ya shawarci 'yan kasuwa masu tasowa da su mayar da hankali kan kasuwancinsu

Attajirin ɗan kasuwar ya kuma bayar da muhimmiyar shawara ga 'yan kasuwa masu tasowa kan yadda za su kula da harkokin kasuwancinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace wata ɗabi'a ce ta da yawa daga 'yan kasuwa masu tasowa a Afrika, kashe kuɗaɗe na ribar da ake samu a cikin kasuwanci fiye da ƙima.

A cewarsa:

"Da zarar ka fara kasuwanci kuma ya kasance ya fara kawo kuɗi, maimakon ka ci gaba da mayar da ribar cikin kasuwancin, sai kawai ka fara kashe kuɗin da tunanin cewa ribar za ta ci gaba da zuwa."

Dangote ya ƙara da cewa akwai ƙalubale da mutum zai fuskanta a kasuwanci, don haka ya zama wajibi ya tsaya ya yi nazarin abubuwan da ya kamata ya yi.

Kara karanta wannan

Masu Yaɗa Jita-Jitar Gwamnan APC Ya Mutu Sun Shiga Uku, Gaskiya Ta Yi Halinta

Dangote ya ce kayayyakin alatu na hana mutum mayar da hankali kan kasuwancinsa

Ya ƙara da cewa mallakar kayayyaki na alatu na iya kawarwa mutum da hankali daga kan abubuwan da suka kamace shi da ya riƙe.

Dangote ya ce kayayyakin alatu na cinye lokacin mutum wajen hana shi mai da hankali kan kasuwancinsa.

Ya ce:

“Ba ni da gida a ko'ina amma na san mutanen da ke yi mun aiki da suke da gida a Landan. Amma ni bani da shi."

Har yanzu Dangote ne ya fi kowa kudi a Afrika

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan cewa har yanzu shugaban rukunin masana'antu na Dangote, Alhaji Aliko Dangote ne ke rike da kundin wanda ya fi kowa kudi a Afrika.

Shafin kiddidigar dukiyar manyan attajira wato Bloomberg, ya bayyana cewa Dangote na da tarin dukiya da ta kai dalar Amurka, biliyan 15.6.

Asali: Legit.ng

Online view pixel