Ikon Allah: An Tsinci Jariri Goye a Bayan Mahaifiyarsa Sa'o'i 24 Bayan 'Yan Bindiga Sun Halaka Ta

Ikon Allah: An Tsinci Jariri Goye a Bayan Mahaifiyarsa Sa'o'i 24 Bayan 'Yan Bindiga Sun Halaka Ta

  • An tsinci wani jariri goye a bayan mahaifiyarsa yana ta sharar barcinsa sa'o'i 24 bayan ƴan bindiga sun halaka ta
  • Ƴan bindigan dai sun tare titin hanyar Pandogari-Allawa ne a jihar Niger inda suka halaka mutum shida nan ta ke
  • Daga cikin waɗanda ƴan bindigan suka halaka har da wata ɗalibar sakandire wacce ke komawa zuwa gida domin hutun Sallah

Jihar Niger - An tsinci wani jariri ɗan wata bakwai a duniya mai suna Habibu, yana barci a bayan mahaifiyarsa sa'o'i 24 bayan ƴan bindiga sun halaka ta a titin hanyar Pandogari-Allawa cikin ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Niger.

Ƴan bindigan dai sun tare titin hanyar Pandogari-Allawa ana gobe Sallah sannan suka harbi fasinjoji shida, ciki har da wata ɗalibar SS2 a makarantar sakandiren mata ta Maryam Babangida da ke a Minna, Hauwa Aliyu, da mahaifiyar jaririn.

Kara karanta wannan

"Ina Kaunar Mijina Duk da Yana Bugu Na Kamar Jaka" Wata Mata Ta Nemi Saki a Kotun Musulunci, Ta Gindaya Sharaɗi 1

An tsinci jariri bayan yan bindiga sun kashe mahaifiyarsa
Jaririn da aka tsinto Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Ƴan sakai suka tsinto jaririn bayan sun je ɗauko gawarwakin mutanen da aka kashe

Shugaban ƙungiyar matasan Lakpma Youth Assembly, Jibril Allawa, ya gayawa jaridar Daily Trust cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Cikin ikon Allah jaririn yana daga cikin waɗanda suka tsira daga harin wanda aka kashe mutum shida. Ƴan sakai da suka je wajen domin ɗauko gawarwakin mutanen sun tsince jaririn yana ta barci a bayan mahaifiyarsa."
"Lamarin ya auku ne a ranar 27 ga watan Yuni, inda mutum shida suka rasa ransu. Maryam ta kiramu ta sanar da mu cewa za ta dawo gida Sallah. Mun gaya mata ta zauna ta yi bikin Sallah a makaranta amma tace ita tana son ta dawo gida ta yi Sallah tare da mu."
"Wani ƙaramin yaro mai Abubakar Ismail, mai shekara 16, wanda ya samu rauni a ƙirjinsa ya samu ruga kafin a ceto shi inda yanzu haka yake asibiti ana duba lafiyarsa."

Kara karanta wannan

Bello Turji Ya Sako Mutum 20 Da Yaransa Suka Yi Garkuwa Da Su, An Bayyana Dalili 1 Da Yasa Yayi Hakan

Shehu Sani Ya Yi Gargadi Kan Tattaunawa Da 'Yan Bindiga

A wani labarin kuma, tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan batun tattaunawa da tsagerun ƴan bindiga.

Tsohon Sanatan ya bayyana cewa tattaunawa da ƴan bindiga ɓata lokaci ne kawai domin ba zai haifarwa ƙasar nan ɗa mai ido ba. Ya jero dalilai uku da suka sanya tattaunawar ba za ta yi amfani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng