'Yan Twitter Za Su Gamu da Takunkumin Takaita Adadin Rubutun da Za Su Ke Gani a Manhajar, Elon Musk

'Yan Twitter Za Su Gamu da Takunkumin Takaita Adadin Rubutun da Za Su Ke Gani a Manhajar, Elon Musk

  • Mai kamfanin Twitter ya kara zuwa da sabon batu, inda yace zai sanya tankunkumi ga masu amfani da manhajar
  • A cewar Elon Musk, hakan zai ba shi damar kula da bayanai da kuma yadda ake tafiyar da tsarin manhajar
  • Ba wannan ne karon farko ba da Musk ke yin sauye-sauye a manhajar ta Twitter ba, ya yi hakan sai da yawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Amurka - Elon Musk, hamshakin attajirin da ya kafa kamfanin Tesla, ya ce ya sanya takunkumi ga adadin sakonnin da masu amfani da shafin Twitter za su iya karantawa a kullum.

A cewarsa, yunkurin zai yi aiki ne don magance batutuwan da suka shafi "tafiyar da bayanai da tsarin", kamar yadda ya bayyana shafinsa na Twitter a yau Asabar 1 ga watan Yului.

Kara karanta wannan

Dakyar na sha: Da jini na ya hau idan na fadi zaben sanata, tsohon shugaban APC ya magantu

Ya ce masu amfani da Twitter wadanda ke da assun da aka tantance sahihancinsu (verified) za su sami damar karanta rubutu 6,000 a kullum.

Elon Musk ya sake kawo sabon tsari a Twitter
Yadda ake samun sauyi a kamfanin Twitter | Hoto: Chesnot/Getty Images
Asali: Getty Images

Sai kuma wadanda gama gari ne (unverified) za a bar su da ganin adadin rubutun Twitter 600 da 300, bi da bi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yaushe wannan tsarin na Twitter zai fara aiki?

Sai dai, Musk bai bayyana lokacin da takunkumin na wucin gadi zai fara aiki ba da kuma tsawon lokacin da zai kare.

Ya rubuta cewa:

"Don magance tsauraran matakan goge bayanan da tafiyar tsari, mun kawo iyakokin wucin gadi kamar haka:
“Asusun da aka tantance ingancinsa zai karanta adadin rubutu 6,000 a kowace rana. Wadanda ba a tantance asusunsu ba kuwa rubutu 600 a kowace rana. Sabbin asusun da ba a tantance su za su karanta 300 a kowace rana."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fitaccen malamin addini a Najeriya ya fadi a filin jirgin sama saboda tsananin rashin lafiya

Ana yawan samun sauyi a shafin Twitter

A cikin wani sakon Twitter mai alaka da wannan, hamshakin attajirin ya kara da cewa zai kara adadin rubutun da kaso 33% nan gaba.

Tun da ya siya kamfanin Twitter, Elon Musk ke ci gaba da yin sauye-sauye a bangarori daban-daban na kamfanin.

'Yan Twitter sun more, Elon Musk zai fara raba musu kudi, amma da sharadi

A wani labarin, Twitter, fitacciyar kafar sada zumunta, na shirin gabatar da wani sabon shirin da zai bai wa jama'ar da ke da dangwalen 'verification' damar samun kudi a kafar.

Elon Musk, mamallakin kamfanin da ya saye shi a watan Oktoban bara ne ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A cewarsa, ana sa ran zubin farko na kudin da zai biya zai kai kusan dala miliyan 5 wanda ya kai kimanin Naira biliyan 2.3.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.