Shugaba Kasar Guinea Bissau Ya Ziyarci Tinubu a Legas, Ya Samu Tarbar Manyan Jiga-Jigan Najeriya

Shugaba Kasar Guinea Bissau Ya Ziyarci Tinubu a Legas, Ya Samu Tarbar Manyan Jiga-Jigan Najeriya

  • Labarin da ke iso mu ya ce, Shugaban kasa Tinubu ya yi ganawar sirri da Shugaban kasar Guinea Bissau a birnin Legas
  • An ruwaito cewa, shugaban ya tarbi Umaro Embalo a Legas tare da wasu manyan ‘yan Najeriya a birnin
  • Ya zuwa yanzu, ba a bayyana gaskiyar abin da suka tattauna a kai ba, amma ana kyautata zaton zaman na da alaka da ci gaban kasashen biyu

Jihar Legas - Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu a a yanzu haka yana ganawa da Shugaban kasar Guinea Bissau kuma Shugaban Shugabannin kasashe a karkashin kungiyar ECOWAS, Umaro Sissoco Embalo a birnin Legas.

Gidan talabijin na Najeriya (NTA) ne ya fitar da labarin ganawar Shugabannin biyu yayin da ya yada wani gajeren bidiyo a shafin Twitter.

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana manufar wannan ganawar ba, kasancewar bayanai basu fito balo-balo ba game da tattaunawarsu.

Kara karanta wannan

FG Na Fuskantar Matsin Lamba Yayin da Aka Nemi Ta Dokubo Kan Barazanar Da Ya Yi Wa Inyamurai

Tinubu da shugaban kasar Guinea Bissau
Ganawar Tinubu da Umaro Embalo | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kalli bidiyon:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu na hutun Sallah a Legas

Tun bayan da Tinubu ya dawo daga birnin Landan a ranar Talata, yana ci gaba da zaman hutun Sallah a jiharsa ta Legas.

Ziyarar da Embalo ya kawo wa Tinubu ce ta farko da wani Shugaba daga nahiyar Afrika ya taba kawo wa Najeriya tun bayan da Tinubu ya karbi ragamar Najeriya.

Yadda Tinubu ya gana da Jonathan kan batun Afrika da ECOWAS

Game da lamuran da suka shafi Afrika da ECOWAS, Tinubu ya gana da tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan don tattauna wasu batutuwa masu muhimmanci.

A ziyarar, Jonathan ya ce ya gana da Tinubu domin labarta masa halin da ake ciki game da nahiyar ta Afrika, rahoton Channels Tv.

A cewarsa yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da Tinubu a gidan gwamnati a Abuja:

Kara karanta wannan

Manyan Abubuwa 5 Da Shugaba Tinubu Ya Aiwatar a Watansa Na Farko a Ofis

"Na zo ne don labartawa sShugaban kasa wasu batutuwa da suka shafi shiyya da da sauran bangarorinta."

Shugaba Tinubu ya gana da Buhari a Landan

A wani labarin, Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon shugaban kasan da ya gabace shi, Muhammadu Buhari, a birnin Landan na kasar Burtaniya.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa har yanzu ba bu wanda ya san sakamakon zaman manyan jiga-jigan biyu saboda har kawo yanzu ba a fitar da sanarwa kan abinda suka tattauna ba.

Sai dai a halin yanzu wasu daga cikin hadiman shugaban kasa sun wallafa Hotunan taron a soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.