Jerin Sunayen Sabbin Kwamishinonin Yan Sanda da Aka Tura Jihohi 8
- Hukumar jin daɗin 'yan sanda ta ƙasa ta amince da tura sabbin kwamishinonin 'yan sanda zuwa jihohi 8 a Najeriya
- Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ya fitar ranar Jumu'a, 30 ga watan Yuni, 2023
- Sanarwan ya bayyana jihohin da suka samu sabbin kwamishinonin, wanda ya haɗa da Borno, Kebbi, Imo, Anambra, Oyo, Ebonyi, Kwara da Ogun
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Hukumar jin daɗin 'yan sandan Najeriya (PSC) ta amince da tura sabbin kwamishinoni zuwa rassan hukumar 'yan sanda a jihohi takwas, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar PSC, Ikechukwu Ani, shi ne ya bayyana tura sabbin kwamishinonin a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 30 ga watan Yuni, 2023.
Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa jihohin da suka samu sabbin kwamishinonin 'jami'an 'yan sanda sun ƙunshi, Borno, Kwara, Oyo, Kebbi, Ebonyi, Ogun, Anambra, da kuma Imo.
Hukumar ta yaba wa sabon mukaddashin sifetan 'yan sanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, bisa natsuwa da kiyaye jinsi wajen tura waɗanda suka dace da muƙaman, This Day ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban hukumar jin daɗin 'yan sanda na ƙasa, Solomon Arase, ya buƙaci sabon muƙaddashin IGP ya riƙa la'akari da illar shiyyoyin ƙasar nan yayin tura sunayen waɗan da ya dace ga PSC.
Jerin sunayen sabbin kwamishinonin 'yan sanda da kuma jihohin da za su jagoranta
Mun haɗa muku jerin sunayen sabbin kwamishinonin jami'an yan sanda da kuma jihohin da zasu jagoranta, ga su kamar haka:
1. Godwin Aghaulor - jihar Borno
2. Adelesi E. Oluwarotimi - jihar Kwara
3. Adebola Ayinde Hamzat - jihar Oyo
4. Augustina Ogbodo - jihar Ebonyi
5. Samuel Titus Musa - jihar Kebbi
6. Aderemi Adeoye - jihar Anambra
7. Stephen Olarewaju - jihar Imo
8. Alamatu Abiodun - jihar Ogun.
Falana Ya Bukaci DSS Ta Hanzarta Bincike, Ta Gurfanar da Bawa da Emefiele a Kotu
A wani labarin na daban mun kawo muku cewa Femi Falana, babban lauya mai fafutukar kare hakkin ɗan adam ya buƙaci DSS ta gaggauta kammala bincike kan Bawa da Emefiele.
Falana ya roƙi hukumar DSS ta gurfanar da mutanen biyu idan ta gano cewa suna da hannu a tuhume-tuhumen da ake masu.
Asali: Legit.ng