Hajjin 2023: Maniyaciyyar Abuja Ta Riga Mu Gidan Gaskiya A Saudiyya
- Hukumar Alhazai a birnin Tarayyar Nigeria, Abuja ta sanar da rasuwar daya daga cikin mahajjata daga birnin
- Abubakar Evuti, daraktan hukumar a birnin, shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu a ranar Juma'a 30 ga watan Yuni
- A karshe ya mika sakon ta'aziya ga iyalan marigayiyar inda ya roke su da su jure wannan rashin da daukar hakan kaddara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Daga daga cikin maniyyatan Babban Birnin Tarayyar Nigeria, Abuja ta riga mu gidan gaskiya a Saudiyya.
Marigayiyar mai suna Hajiya Amina Yunusa ta rasu ne a Makkah da ke kasar Saudiyya.
Daraktan Hukumar Alhazai a birnin Tarayya, Malam Abubakar Evuti shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu a ranar Juma'a 30 ga watan Yuni.
Ya bayyana rasuwar daya daga cikin mahajjatan a Saudiyya
Evuti ya yi addu'ar Allah madaukakin sarki ya yi wa Hajiya Amina rahama, ya yafe mata kurakurenta kuma ya sa ta huta, Vanguard ta tattaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa:
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Hukumar Alhazai ta birnin Tarayya Abuja, ta na sanar da rasuwar Hajiya Amina Yunusa.
"Muna fatan Allah ya yafe mata kurakurenta, ya karbi ibadunta, ya kuma sa aljannar firdausi ce makomarta."
Daraktan ya mika sakon ta'aziya ga iyalanta inda ya ba su hakuri
Pulse ta tattaro Daraktan na mika sakon ta'aziya ga iyalan marigayiyar inda ya shawarce su da su dauki hakan a matsayin kaddara wanda babu makawa sai ta faru da ita.
Ya kara da cewa:
"Ya kamata mu dauki hakuri ganin yadda ta rasu a birnin Makkah mai tsarki bayan gama aikin hajji karbabbiya.
Hajji karbabbiya sakamakonta gidan aljannar firdausi ce kamar yadda hadisan Annabi Muhammad (SAW) suka tabbatar."
Gwamnan Bauchi Ya Ba Da Kyautar Kudi Ga Alhazai 3000 A Saudiyya
A wani labarin, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya gwangwaje mahajjata fiye da 3,000 daga jihar da kyautar kudade.
Limaman Kiristoci A Arewacin Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Kona Alkur'ani A Sweden, Sun Bayyana Mataki Na Gaba
Gwamnan ya ba wa ko wane mahajjaci Riyal 300 kwatankwacin kudin Najeriya N75,000 a Saudiyya yayin kai ziyara a sansaninsu.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai, Mukhtar Gidado ya sanya wa hannu a ranar 30 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng