Gwamnan Bauchi Ya Gwangwaje Alhazai 3000 Da Kyautar Makudan Kudade A Saudiyya

Gwamnan Bauchi Ya Gwangwaje Alhazai 3000 Da Kyautar Makudan Kudade A Saudiyya

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya gwangwaje mahajjata fiye da 3000 da kudade a kasar Saudiyya
  • Gwamnan ya ce ya yi haka ne don rage musu radadin kudaden da suke kashewa yayin zamansu a Saudiyya
  • Ya roki maniyyatan da kada su gajiya wurin yi wa gwamnatinsa addu'a da jihar Bauchi da ma kasa baki daya

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ba wa mahajjata fiye da 3000 Riyal 300 ga ko wannensu a Saudiyya.

Wannan na dauke ne a cikin wata sanarwa da mai ba wa gwamnan shawara akan yada labarai, Mukhtar Gidado ya sanya wa hannu a ranar Juma'a 30 ga watan Yuni.

Bala Mohammed Ya Gwangwaje Alhazan Bauchi 3000 Da Kyautar Kudade A Saudiyya
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Moohammed. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Gidado ya ce gwamnan ya ba da wannan kyauta ne yayin kai ziyara a sansanin 'yan jihar Bauchi a Saudiyya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Hajj 2023: Fitaccen Gwamnan Jihar Arewa Ya Jagoranci Mahajjata Musulmi Sallah A Makka

Gwamnan ya ba wa alhazan ne don rage musu radadi a Saudiyya

Daily Trust ta tattaro cewa Riyal 300 ya kai kudin Najeriya N75,000.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gidado ya ce gwamnan ya ba da wannan kyauta ne don rage wa alhazan radadin kashe kudade yayin zamansu a kasa mai tsarki.

Ya kara da cewa gwamnan ya yabi sansanin 'yan jihar a Muna ganin yadda suka nuna halin kwarai Saudiyya.

A cewarsa:

"Mohammed ya yabe su saboda mutunta hukumomi a Najeriya da kuma kasar Saudiyya.
"Ya musu alkawarin ci gaba da ba wa hukumar alhazai a jihar goyon baya don samun ingantaccen jigilar mahajjata."

Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da ba da gudumawa ga hukumar alhazai

Gidado ya ce hukumar alhazai ta jihar za ta hada karfi da hukumar a matakin kasa don shawo kan matsalolin da aka fuskanta a kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Ba Ka da Tausayi: Peter Obi Ya Tsoma Baki a Rusau Din Kanawa, Ya Yi Wa Abba Gida Gida Kaca-Kaca

Ya ce gwamnan ya godewa mahajjata a jihar bisa addu'o'in da suke yi wa gwamnatinsa, inda ya bukace su da su ci gaba da hakan.

Bauchi Ta Yi Babban Rashi Yayin Da Farfesa Abdu Ibrahim Ya Kwanta Dama

A wani labarin, jihar Bauchi ta yi babban rashi yayin da Farfesa Ibrahim Abdu ya kwanta dama.

Mai girma gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed ya yi alhinin mutuwar wannan Farfesa inda ya ce ya ba wa jihar dama kasa baki daya gudumawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.