Dalilinmu Na Ruguza Wasu Gine-Gine a Jihar Kano – Abba Bai Yi Nadamar Komai ba
- Abba Kabir Yusuf ya hadu da Sarkin Kano da ‘yan majalisarsa a ranar hawan dashe a gidan Gwamnati
- Sabon Gwamnan na jihar Kano ya ce yana rusa gine-gine ne saboda an saida filaye ba kan ka’ida ba
- Abba Gida gida ya shaidawa Sarki Aminu Ado Bayero irin nasarorin da ya samu a cikin watansa na farko
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Abba Kabir Yusuf ya ce bai da nadama a game da ruguje-rugujen da yake yi da kuma abin da ya kira karbe kadarorin gwamnatin jihar Kano.
Vanguard ta ce Abba Kabir Yusuf ya yi wannan bayani ne a lokacin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da ‘yan majalisarsa su ka kai ziyara.
Tawagar Mai martaba da ta je gidan gwamna a jiya ta hada da daukacin Hakiman cikin birnin Kano. Idan za a tuna a yau ne ake hawa Nasarawa.
A wani jawabi da ya fito daga bakin Mai magana da yawun Gwamnan Kano, Hisham Habib, ya ce Abba Kabir Yusuf ya fadi hikimar yin rushe-rushe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Mai girma Gwamna, tsohuwar gwamnati ta rika saida filaye ba a kan ka’ida ba, ya ce ya zama dole su karbe filayen, su dawo hannun Kanawa.
Jawabin Gwamna Abba Kabir Yusuf
Mai Martaba, ya na da muhimmanci masarauta ta sani cewa mu na rusa gine-gine ne domin karbar kadarorin gwamnati da aka mallaka ba daidai ba
Kuma za mu tabbata mun karbe irin wadannan kadarori domin su amfani mutanen kirkin Kano.
- Abba Kabir Yusuf
Legit.ng Hausa ta samu labari Gwamna Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya ce rushe-rushen zai taimakawa wajen kara kimar masarauta.
Gwamnatin NNPP ta samu nasarori
Da yake bayanin nasarorin da ya samu a watan farko, Gwamnan ya yi bayanin yadda ya kashe Naira Biliyan 1.5 a biyawa dalibai 55, 000 kudin NECO.
Abba Gida Gida ya ce an fara rage yawan sace-sacen wayoyi bayan haskaka titunan cikin birni, sannan ana kokarin biyan albashi da fansho a kan kari.
Daga cikin nasarorin gwamnatin NNPP kamar yadda Gwamnan ya fada akwai shirin tantance yaran Kano da za a tura zuwa karo karatu a jami’o’in waje.
Akwai abin dubawa Inji Sipikin
Da mu ka yi magana da Mukhtar Mudi Sipikin, ya shaida mana cewa a ra'ayinsa akwai gine-ginen da bai kamata a rusa su ba duk sun saba ka'ida.
Tsohon 'dan takaran majalisan na Fagge ya bada misali da gine-gine da aka yi a Kofar Na Isa, yake cewa rushe-rushe za su karya tattalin arziki.
A game da gini a kan badala kuwa, matashin 'dan siyasar ya ce ginin da aka yi sun inganta tsawo, sun yi maganin masu shaye-shaye a yankunan.
Wata Sabuwa: Babban Dan Kwankwasiyya Ya Soki Rusau Da Abba Gida Gida Ke Yi A Kano, Ya Ce Ba Daidai Ba Ne
Kudin wutar lantarki zai tashi
Da alama saura kiris a ba kamfanonin raba lantarki damar su kara farashi a fadin kasar nan. Rahoto ya zo cewa ana jiran sa hannun shugaban kasa.
Hukumar NERC za ta zauna da Bola Tinubu a Aso Rock domin neman amincewarsa wajen canza farashin wuta a dalilin tashin Dalar Amurka a yanzu.
Asali: Legit.ng