Kotu Ta Tasa Keyar Yaro Mai Shekaru 18 Zuwa Gidan Kaso Kan Zargin Satar Akuya a Jihar Arewa, An Masa Sassauci

Kotu Ta Tasa Keyar Yaro Mai Shekaru 18 Zuwa Gidan Kaso Kan Zargin Satar Akuya a Jihar Arewa, An Masa Sassauci

  • Kotun yanki da ke jihar Plateau ta daure matashi mai shekaru 18 bisa zargin satar akuya a cikin gonar wani mutum
  • Wanda ake zargin mai suna Ibrahim Ali ya saci akuyar ce a gonan wani mutum mai suna John Dung da ke Jos
  • Alkalin kotun ya ba shi zabin biyan tara na N10,000 da kuma biyan diyya N20,000 ko watanni uku a gidan kaso

Jihar Plateau - Kotun yanki da ke zamanta a jihar Plateau ta daure wani matashi watanni uku a gidan gyaran hali bisa zargin satar akuya.

Wanda ake zargin mai suna Ibrahim Ali mai shekaru 18 ya saci akuyar ce da akalla kudinta ya kai har N20,000.

Kotu ta daure yaro mai shekaru 18 a gidan kaso bisa zargin satar akuya a gona
Kotun Ta Ba Wa Matashin Zabi Yayin Yanke Hukuncin. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Alkalin kotun, Shawomi Bokkos ya daure Ali Ibrahim bayan ya amince da dukkan zargin da ake tuhumarsa akai.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Peter Obi Ya Zauna da Musulmai, Ya Ba Su Kudi a Gyara Masallatai

Matashin ya roki kotu ta masa sassauci yayin yanke hukuncin

Ali Ibrahim ya kuma roki alkalin kotun da ya yi masa sassauci yayin yanke hukuncin, Daily Trust ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkalin kotun har ila yau, ya umarci wanda ake zargin zabin biyan N10,000 da kuma biyan diyya N20,000 ga mai karar ko kuma zaman watanni a gidan gyaran hali kan saba doka.

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Monday Dabit ya fadawa kotu cewa an kai rahoton satar akuyan a ofishin yanki na 'yan sanda da ke Rantya.

An bayyana yadda yaron ya sace akuyar a cikin gona

Mai karar, Mista John Dung ya kai rahoton a ranar 5 ga watan Afrilu na wannan shekara bisa zargin wuce gona da iri da kuma satar akuya a cikin gonarsa.

Kara karanta wannan

Kotun Shari'ar Musulunci A Kano Ta Tisa Keyar Wani Lauyan Bogi Zuwa Gidan Kaso, Ta Bashi Shawara Mai Muhimmanci

Mai gabatar da karar ya kara da cewa yayin binciken 'yan sanda, wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin da ake tuhumarsa akai, cewar The Nation.

Ya kara da cewa aikata hakan ya sabawa dokokin hukunce-hukunce ta jihar Plateau.

Kano: Kotun Shari'ar Musulunci Ta Daure Lauyan Bogi Watanni 15 A Gidan Gyaran Hali

A wani labarin, kotun shari'ar Musulunci a Kano ta daure lauyan bogi watanni 15 a gidan kaso.

Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru ta daure Zaharaddin Sani bisa zargin cin amana da damfara.

Alkalin kotun, Abdulmuminu Gwarzo ya ce wanda ake zargin ya kuma bayyana kanshi a matsayin dan jarida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.