Za Ayi Sallah da Aljihu a Cike, Gwamnatin Kano Ta Biya Fansho da Albashi Babu Giɓi
- Tun kafin watan Yuni ya cika, Gwamnatin Jihar Kano ta biya albashin ma’aikatan gwamnati
- Abin da ya jawo mutane su ke farin ciki shi ne albashin ya zo a daidai lokacin da ake shirin sallah
- An biya fansho da giratuti na watan Yuni, kuma ba ayi wa kudin gibi kamar yadda aka saba ba
Kano - Ana jaji-birin sallah ne Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biya ma’aikatan jihar Kano albashinsu ba tare da an zaftare masu sisin kobo ba.
Baya ga ma’aikatan gwamnatin jihar, Daily Post ta ce an biya tsofaffin ma’aikata da suka yi ritaya fanshonsu, hakan ya jawo su ke cike da murna.
Wannan ne cikakken albashin farko da aka biya a jihar a karkashin jagorancin Abba Yusuf, a baya ana zargin an rika rage wani kaso na albashin.
Zauren 'Yan fansho ya yaba
Shugaban kungiyar ‘yan fansho na jihar Kano, Alhaji Ado Ibrahim ya shaida cewa ba su taba ganin irin haka ba, ya na rokon a cigaba da tafiya a haka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ibrahim ya fadawa jaridar cewa ya zama dole a yabawa gwamnati domin bayan hakkinsu da su ka fito, ba a cire masu ko sisi kamar yadda aka saba ba.
"Ya zama tilas mu jinjina, domin an biya kudin fansho kafin karshen wata, sannan ba a zaftare ko kobo kamar yadda aka saba yi a can baya ba."
- Shugaban zauren 'yan fansho
A wani rahoton, an ji cewa kungiyar ‘yan fanshon ta nemi alfarmar sabuwar gwamnati ta rika biyan hakkokin matattu da wadanda su ka bar aiki.
Wani ma’aikaci a ma’aikatar ilmi ta jihar Kano ya tabbatar da haka a shafin Facebook, ya ce:
Eid El Kabir: Portable Mai Wakar Zazu Ya Hargista Intanet Bayan Nuna Shanu 5 Da Raguna 2 Da Ya Siya Don Shagulgulan Sallah
“Na rantse da girman Allah tun tsawon shekara takwas, sai a wannan watan (June) naga albashi na cikakke.”
Shi ma wani jami’i mai goyon bayan gwamnatin APC ya nuna NNPP ta ba su mamaki, ya rubuta:
“A gaskiya mu APC Kano munji kunya Gwanatin Abba ta biya mu pension ba yanka.”
A cewar wani Ismail Nasiru a Facebook, an biya su albashin watan Yuni ba tare da wani gibi ko zaftare ba.
Shi kuma wani Bawan Allah ya yi farin ciki da yadda sabon Gwamna ya waiwayi tsofaffin, an biya iyayensa fanshonsu na watan nan.
A madadin Iyayenmu ‘Ƴan Fansho, muna Godiya ga Mai Girma Gwamnan jihar Kano.
An dakatar da albashin wasu
Yayin da ma’aikata da ‘yan fansho su ke farin ciki, ma’aikatan da Abdullahi Umar Ganduje ya dauka a kurarren lokaci ba su samu kudinsu ba.
An ji labari Gwamnati ta bada umarni a dakatar da albashin sababbin ma’aikatan, sai an yi cikakken bincike a kan yadda aka dauke su tun farko.
Asali: Legit.ng