Takaitaccen Bayani Kan Hawan Sallah A Masarautun Daura Da Katsina
- Bikin hawan sallah a ƙasar Hausa biki ne mai ɗumbin tarihi da aka ɗauki lokaci mai tsawo ana gudanar da shi
- A lokacin bukukuwan hawan, sarakunan gargajiya da jama'arsu kan fito cikin kwalliya irin ta gargajiya
- A lokutan bukukuwan sallah, ana gudanar da hawa guda biyu ne a masarautar Katsina da kuma ta Daura
Katsina - Bikin hawan sallah biki ne mai ɗumbin tarihi da manyan masarautu a ƙasar Hausa ke gudanarwa a lokutan shagulgulan karama ko babbar sallah.
Ana alaƙanta hawan dawakai da ake yi a lokutan shagulgula da nuna ƙarfin mayaƙa, da kuma shirin yaƙi wanda ya samo asali tun a can baya lokacin da ake yaƙe-yaƙe.
A masarautar Katsina da kuma masarautar Daura, akan gudanar da hawa guda bibbiyu ne a kowace sallah.
Takaitaccen bayani kan bikin hawan sallah a Daura
Bikin hawan daba, ko bikin sallah na Daura, biki ne da ake gudanarwa duk shekara a cikin garin Daura da ke jihar Katsina Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sarkin Daura ne ke gudanar da bikin a lokacin ƙaramar sallah da kuma lokacin babbar sallah. A kan gudanar da bikin a lokacin maulidi ma.
Ana yin bikin ne ta hanyar gabatar da fareti na mahaya dawakai, wadanda suke sanye da kayan gargajiya na gidan sarauta.
Legit.ng ta samu zantawa da wani mamba a tawagar hakimin 'Yanduna, mai suna Salisu Yusuf, dangane da yadda ake gudanar da bukukuwan sallah a masarautar.
Bikin sallar Daura a cewarsa:
“zai fara ne daga ranar jajiberin sallah, wato ranar Talata 27 ga watan Yunin da muke ciki. A wannan rana, hakimai za su shigo cikin garin Daura daga sassa daban-daban na masarautar.”
“A ranar ne Sarki ya ke amsar Jafi. Yadda abin yake shi ne duk wani hakimi idan ya shigo, kai tsaye zai zarce fadar mai martaba sarkin Daura, domin ya kai gaisuwa.”
Ya bayyana cewa magatakardan fadar ne ke ɗaukar sunayen duk hakiman da suka zo, da kuma lokacin da suka iso.
Hawan Sallah
A rana ta biyu, wato ranar Laraba 28 ga watan Yunin 2023, hakiman da suka zo za su fara taruwa a gidan Sarkin Daura tun daga misalin ƙarfe 8 na safe har zuwa ƙarfe 9:30 na safe.
Salisu ya bayyana cewa hakiman ne za su zauna su fitar da tsarukan ina za a bi a yayin hawan.
Daga nan sarki zai fito, sai a rankaya a tafi zuwa masallacin Idi a kan dawakai.
A kalaman salisu:
"Da zarar an kammala sallar Idin, an kammala huɗuba, sarki da mutanensa za su tafi zuwa gidan tarbar baki, wanda anan ne mai martaba Sarkin Daura zai ci abinci tare da bakin da suka zo."
Ya kara da cewa daga nan kuma za a hau dawakai, inda sarki zai kewayo ta bayan gari zuwa fada ta kofar yamma, wacce ake kira da Kofar Sarki Abdulrahman.
Bayan wannan mai martaba sarki zai amshi gaisuwa daga hakimai da sauran manyan baki, inda daga nan ne magatakardan masarautar zai gabatar da jawabin godiya na mai martaba, sai a sallami kowa, shikenan hawan sallah, kuma hawa na farko ya ƙare.
Hawan Magajiya
A rana ta 3 kuma, wato ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, sarkin Daura zai gabatar da hawan magajiya.
Galadima zai tashi da safe ya tafi zuwa gidan Magajiya, wacce sarauta ce mai muhimmanci a masarautar ta Daura.
Idan Galadima ya gama tabbatar da cewa an gama shirya komai, zai zo ya shaidawa sarki, wanda daga nan zai tafi zuwa gidan na Magajiya domin kai gaisuwa.
Salisu ya ce:
"Wannan al'ada ce ta cewa sarki zai ce ya gaishe da Magajiya, ko da wacece kuwa ke rike da sarautar."
"Don akwai lokacin sarkin Daura Bashar, da ya zamto cewa magajiyar ma 'yarsa ce, amma haka nan ya kai gaisuwa tunda al'ada ce."
A yayin gaisuwar, sarki zai bai wa magajiyar goro, turare, atamfa da sauran wasu abubuwa na al'ada.
Bayan fitowa daga gidan nan Magajiya, sarki zai wuce kudancin garin, inda nan ma zai zagayo ta wasu muhimman ƙofofi, kafin daga bisani ya sake komawa fada.
Hakimai da sauran masu riƙe da muƙaman gargajiya za su zo su kawo gaisuwa, bayan kammala wannan, sai sarki ya yi jawabi, sai a sallami kowa da kowa.
Hawan Sallah a Katsina
Ana gudanar da hawan sallar Katsina ne a lokutan ƙarama da na babbar sallah. Ana fara hawan ne da safiyar ranar sallah, inda sarki da tawagarsa suke hawa a kan dawakai zuwa masallacin Idi, kamar yadda BBC ta tattaro.
Sarkin zai bi ta Kofar Guga zuwa masallacin Idi. Bayan kammala sallar Idi, sarki zai zagaya ta hanyar Kofar 'Yan ɗaka zuwa Filin Kangiwa, inda za a gudanar da jawabai a gaban manyan jihar Katsina, ciki kuwa hadda mai girma gwamnan jihar.
Eid El Kabir: Portable Mai Wakar Zazu Ya Hargista Intanet Bayan Nuna Shanu 5 Da Raguna 2 Da Ya Siya Don Shagulgulan Sallah
Washe garin sallah, Sarkin Katsina yana gabatar da hawa, wanda ake kira da Hawan Bariki, inda hakimai tare da sauran masu sarautun gargajiya suke yin hawa zuwa gidan gwamnati.
A wannan ziyara, sarki da zai gana da gwamna, inda za su gaisa su kuma yi wa juna barka da sallah.
Tsadar dabbobi da kayan masarufi ba zata hana mu yin bikin sallah ba, cewar mazauna Abuja
Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto, inda wasu daga cikin mazauna birnin tarayya Abuja suka bayyana cewa duk da tsadar dabbobi da kayayyakin masarufi, za su gudanar da bikin sallarsu yadda ya samu.
Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa tun tuni suka tanadi abubuwan da suke bukata domin shagulgulan sallah.
Asali: Legit.ng