‘Zagin Annabi’: Shehin Malamin Musulunci Ya Yi Magana Kan Kisan da Aka Yi a Sokoto
- Usman Buda ya kwana a barzahu saboda ana zarginsa da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW)
- A jiya ne mutane su ka aukawa wannan mahauci a abatuwa, kalamansa su ka yi sanadiyyar kashe shi
- Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya na ganin hakan ya nuna irin yadda jahilci ya yi wa mutane katutu
Sokoto - A karshen makon nan wasu mutane su ka hallaka Usman Buda bisa zargin cewa ya yi kalamai na batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Legit.ng Hausa ta fahimci wannan lamari wanda ba shi ne na farko da ya faru a garin Sokoto ba, ya jawo maganganu da-dama daga kusan fadin Najeriya.
Fitaccen malamin nan da yake garin na Sokoto, Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto mni, ya yi amfani da shafinsa na Facebook, ya yi magana a kan batun.
A yammacin Lahadi, Mansur Sokoto ya yi Allah-wadai da wannan kisan kai da aka yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Al'umma na bukatar gyara a yau
Da yake magana da kusan karfe 8:00 na dare a agogon Najeriya, Shehin malamin hadisin Manzon Allah (SAW) ya nuna akwai gyara ta kowane bangare.
Farfesa Mansur Sokoto ya na ganin an kashe wannan mahauci ne saboda jahilcin gama-garin mutane da kuma rashin jajircewar hukumomin kasar nan.
Abin da ya faru a Sokoto yau (Lahadi) abin takaici ne matuka. Jahilai suna bukatar karatu…
Malamai suna bukatar hikima wajen karantar da su, Hukuma tana bukatar jajircewa wajen hana mutane daukar doka a hannu.
'Yan sanda za su yi bincike
Rahoton Punch ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun fara yin bincike a kan abin da ya faru, da nufin a gano masu hannu a laifin domin a hukunta su.
Mai magana da yawun ‘yan sandan reshen Sokoto, Ahmad Rufai ya ce sun samu labari da karfe 9:20 na safe cewa wani Usman Buda ya yi batanci.
A sanadiyyar haka kuma wani da ya ke abatuwan ya aukawa wannan mahauci mutumin Gwandu kafin jami'an tsaro su iya karasowa zuwa wurin.
Ko da DPO na yankin kwanni da tawagarsa su ka isa inda abin ya faru, an wuce da gawar Buda zuwa asibitin UDUTH, wanda ya yi ta’adin kuma ya tsere.
Shirin sallar layyah a Zamfara
A rahoton nan ne aka ji Shugaban APC na reshen jihar Zamfara ya ce Bello Matawalle ya raba masu N200m domin ayi hidimar babbar sallah a makon nan.
Matawalle ne ya jawo wasu ma’aikatan jihar Zamfara ba su karbi albashi tun Fabrairu ba. Sabon Gwamna ya ce N3m ya samu a asusun Gwamnati.
Asali: Legit.ng