Sokoto: Fusatattun Mutane Sun Halaka Matashi Bisa Zargin Batanci Ga Annabin Rahama
- Wasu mutane sun yi ajalin wani mahauci mai suna Usman Buda wanda ake zargin ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW)
- Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin Usman Buda yana siyar da kayan ciki ne a mahautar da ke Sokoto
- Kakakin rundunar 'yan sandar jihar, ASP Ahmed Rufa'i ya tabbatar faruwar lamarin inda ya ce sun dauki gawar zuwa asibiti
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Sokoto - Fusatattun matasa sun yi ajalin wani mahauci mai suna Usman Buda bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).
Lamarin ya faru ne a babban mayanka ta jihar Sokoto da safiyar yau Lahadi 25 ga watan Yuni da misalin karfe 8:00 na safe.
Wani jami'in tsaro da ya bukaci a boye sunansa ya bayyana cewa marigayin yana zama ne a Gidan Igwe da ke karamar hukumar Sokoto ta Arewa.
Ya ce Usman yana siyar da kayan ciki ne a kasuwar kifi da kayan gwari da aka fi sani da Kasuwan Dankure da ke cikin Sokoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng Hausa ta tuntubi wasu mutane akan faruwar lamarin
Da Legit.ng Hausa ta tuntubi wani mazaunin yankin mai suna Surajo Sa'adu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa jami'an tsaro sun dauki gawar zuwa asibiti.
Sannan wani matashi mai suna Ja'afar Usman ya ce tabbas sun isa wurin da lamarin ya faru inda suka ga jami'an tsaro sun dauki gawar marigayin zuwa asibitin UDUTH.
A cewarsa:
"Tabbas hakan ta faru don munje har wurin da abin ya faru inda muka tarar jami'an tsaro sun dauki gawar a motarsu zuwa asibitin koyarwa na UDUTH.
Rundunar 'yan sandan jihar sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 9:20 na safe cewa an kashe Usman Buda kan zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW), Daily Trust ta tattaro.
'Yan sanda sun tabbatar da kashe mahaucin a Sokoto
A cewar kakakin 'yan sanda, ASP Ahmed Rufa'i:
"Bayan samun kiran, Kwamishinan 'yan sanda da babban jami'in dan sandan yankin Kwanni sun jagoranci 'yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru.
"Zuwan 'yan sandan ke da wuya mutanen suka watse yayin da 'yan sanda suka dauke shi zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Usman Danfodio (UDUTH) inda aka tabbatar da mutuwarshi.
"Har ila yau, an fara binciken wadanda suka aikata hakan don gurfanar da su a gaban kotu."
'Batanci: 'Ya'yan Mu Ba Za Su Sake Zuwa Makaranta Ba, Iyayen Deborah Sun Magantu
A wani labarin, mahaifiyar Deborah Samuel, Alheri Samuel ta ce yaransu ba za su sake zuwa makaranta ba.
Alheri ta bayyana haka yayin wata hira da akayi da ita cikin jimami da hawaye saboda kuncin mutuwar Deborah.
Yayin da mahaifinta, Emmanuel Garba ya ce sai da ya biya N120,000 don dauko gawar Deborah zuwa Niger.
Asali: Legit.ng