Na Zaci Kamfanoni Za Su Neme Ni: Mai Digiri Ya Kwaranyo Hawaye Yayin da Ya Kama Sana’ar Kiwon Kifi

Na Zaci Kamfanoni Za Su Neme Ni: Mai Digiri Ya Kwaranyo Hawaye Yayin da Ya Kama Sana’ar Kiwon Kifi

  • Wani matashi dan Najeriya ya tuno da irin karairayi da aka yi masa a lokacin yana dalibin jami’a a Najeriya
  • A cewarsa, an ba shi tabbacin cewa manyan kamfanoni za su zo nemansa ya yi musu aiki bayan kammala karatunsa
  • Sai dai, bayan shekaru da ya kammala karatunsa, matashin ya sake digiri da fannin karatunsa ya kama kiwon kifi

Wani dan Najeriya ya bayyana yadda manya da magabatansa suka yaudare shi a lokacin da yake makaranta a wata jami'ar Najeriya.

A cewarsa, magabatansa sun ce da zarar ya gama makaranta, to tabbas manyan kamfanoni za su zo nemansa ya yi musu aiki.

Bayan ya kammala makaranta, sai ya gane cewa karya ake sharara masa, sai ya yanke shawarar yiwa kansa karatun ta natsu, ya kama noma.

Yadda matashi ya kama sana'ar kiwon kifi
Kiwon kifi na kama bayan kammala jami'a | Hoto: @bigbrosjet/TikTok.
Asali: TikTok

Wani faifan bidiyon da aka yada a TikTok ya nuna lokacin da matashin ke lura da tafkunan kifinsa sannan kuma yana sayar da kifi ga wata ‘yar kasuwa da ta ziyarci gonar.

Kara karanta wannan

"Bayan Wuya": Matashiya Wacce Ke Yawon Talla Ta Koma Turai, Ta Fara Aiki a Matsayin Malamar Asibiti

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Ka gama makaranta tukuna, manyan kamfanoni za su zo nemanka, kun shirga min karya.”

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan TikTok

Bidiyon ya jawo tsokaci da cece-kuce da yawa daga masu amfani da yanar gizo wadanda suka karfafa masa kan aikinsa na kiwon kifi. Ga martanin jama’a:

@callmedavid ya ce:

"Idan kai dan Najeriya ne kuma ba dan gidan masu arziki bane mai manya gara ka koyi sana'a bayan makaranta don tuni dama riga ka rasa 3."

@Bambam ya rubuta:

"Na yi kururuwan wai wace irin rayuwa ce wannan, Allah ya albarkaci hannunka."

@cake_surgeon ya kara da cewa:

"Dan uwa kana yin abin da ya dace, babu wani abu mai kyau da ya wuce zama mai zaman kansa."

@Realeco ya mayar da martani:

"Buga-buga zai ba ka sakamako mai kyau."

@Osaz gizzy ya ce:

Kara karanta wannan

“Aiki Ya Yi Kyau”: Matashi Ya Kammala Hadadden Gidansa, Ya Zuba Kujeru Yan Waje Da Kayan Alatu

@user341343648999 ya ce:

"Najeriya."

@oluwadhice ya rubuta:

"Na rantse karya suka shirga mana."

@namadi yace:

"Wannan lamari ya girgiza ni."

@Phephy00 yayi sharhi:

"Manyan kamfanonin suna kan hanya, suna siyan mai ne."

@Blacky ya mayar da martani:

"Halin da nake ciki a yanzu kenan."

Matashi mara hannuwa ya koyi dinki

A wani labarin, bidiyo ya nuna wani matashin da ke sana'ar dinki duk da nakasar da yake dashi na rashin hannuwa.

A bidiyon da ya yadu, an ga lokacin da matashin ke amfani da dungulmin hannunsa yana dinki, jama'a sun girgiza.

A bangare guda, mutane da yawa sun yi martani mai daukar hankali, sun yaba yadda ya ki kashe zuciyarsa ya yi ta bara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.