JAMB Ta Bayyana Sabon Mafi Karancin Makin Shiga Jami'o'i, Poly da FCE a Najeriya

JAMB Ta Bayyana Sabon Mafi Karancin Makin Shiga Jami'o'i, Poly da FCE a Najeriya

  • Hukumar JAMB ta amince da maki 150 a matsayin mafi karancin makin neman gurbin karatu a jami'o'in Najeriya
  • Farfesa Ishaq Olayede ya bayyana cewa sun amince da 100 a matsayin mafi karancin makin neman gurbi da kwalejojin fasaha da na ilimi
  • Ya kuma gargaɗi kowace makaranta a Najeriya ta zaɓi makin da ya dace amma kar ta kuskura ta gaza mafi ƙarancin da JAMB ta yanke

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta fitar da sabon mafi karancin maki (Cut of mark) na shiga manyan makarantu a zangon 2022/2023.

Daily Trust ta rahoto cewa JAMB ta amince da maki 140 zuwa sama a matsayin mafi karancin makin neman gurbin shiga jami'o'in Najeriya a zangon karatu 2022/2023.

Sabon mafi karancin makin neman gurbi a manyan makarantu.
JAMB Ta Bayyana Sabon Mafi Karancin Makin Shiga Jami'o'i, Poly da FCE a Najeriya Hoto: JAMB

Shugaban JAMB na ƙasa, Farfesa Is-haq Oloyede, ne ya faɗi haka yayin da yake jawabi kan neman gurbin shiga makarantun gaba da Sakandire a wurin taron tsare-tsaren 2023 a Abuja ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Maciji Ya Kashe Hatsabibin Babban Kwamandan ISWAP A Dajin Sambisa

Farfesa Oloyede ya ƙara da cewa hukumar ta kuma amince da maki 100 a matsayin mafi ƙarancin makin neman gurbin shiga kwalejojin fasaha (Poly) da kwalejojin ilimi (FCE) a faɗin ƙasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi bayanin cewa wannan makin da JAMB ta kayyade shi ne mafi ƙaranci, kuma ba tilas bane makarantu su bi, su na ikon ƙarawa ya wuce haka amma kar ya gaza wannan.

Oloyede ya umarci kowace makaranta a faɗin Najeriya ta bi wannan sabon makin, inda ya gargaɗi makarantu cewa karsu kuskura ku gaza wannan mafi ƙarancin makin.

Haka zalika ya ce kowace makaranta ta tabbata ta ɗauki mafi karancin makin da zata duba musamman wajen tantance masu neman gurbi da kuma sakamakon fita daga Sakandire (SSCE).

Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban JAMB na cewa:

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Nuna Takaicinsa Kan Kisan Manoma a Borno, Ya Bayyana Kwakkwaran Matakin Da Zai Dauka

"Dole kowace makaranta ta bi mafi ƙarancin makin da muka yanke, wannan na nufin babu makarantar da zata ɗauki maki ƙasa da haka."
"Game da jami'o'in kuɗi guda 15 da suka roki a basu dama su ɗauki 120 da 130 a matsayin mafi ƙarancin maki, ku sani 140 muka yanke kuma ba zamu yarda a saɓa ba."

Sabbin Hafsoshin Tsaro da IGP Zasu Dawo da Zaman Lafiya a Filato, Mutfwang

A wani labarin kuma Gwamnan Filato ya bayyana yakinin cewa sabbin hafsoshin tsaro zasu kawo karshen kalubalen tsaron da ya addabi ƙasar nan.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya yi zaɓi nagari domin ya zakulo zakaƙuran mutanen da suka cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262