Nadin Mukamai: Gwamnatin Tinubu ta Raba Gardamar OAUTHC, ta Nada Adegbehingbe
- Gwamnatin tarayya ta nada sabon Shugaban rikon kwarya a asibitin koyon aiki na Obafemi Awolowo
- Olayinka Oladiran Adegbehingbe zai jagoranci asibitin na watanni kafin nada cikakken shugabana
- Sanarwar da aka fitar ta nuna Farfesa Olayinka Adegbehingbe ya kware a bangaren kashi da rauni
Osun - Gwamnatin tarayya ta sanar da Olayinka Oladiran Adegbehingbe a matsayin sabon shugaban asibitin koyar da aikin OAUTHC, Ile-Ife a jihar Osun.
Rahoto ya zo a Tribune cewa Farfesa Olayinka Oladiran Adegbehingbe ya zama shugaban rikon kwarya na asibitin na Obafemi Awolowo da ke Osun.
Olayinka Adegbehingbe wanda Farfesa ne a bangaren cututtukan kashi da munanan raunuka ya dare wannan kujera a matsayin babban darektan riko.
Likitan zai yi watanni shida ya na jagorantar asibitin kafin a nada cikakken babban darekta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban rikon kwarya
Sanarwar da ta fito da Darektan kula da ma’aikata na ma’aikatar lafiya ta tarayya ta ce da zarar an gama lalube, za a sanar da cikakken CMD na OAUTHC.
Hassan Sallau ya fitar da wannan sanarwa a ranar Alhamis da ta gabata, a madadin babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya ta Najeriya da ke Abuja.
Wanene sabon CMD?
Adegbehingbe mutumin jihar Ondo ne kuma ya yi karatun digirinsa a jami’ar ta Obafemi Awolowo. Rahoton ya ce ya kammala digirin farko a 1989.
Farfesan ya na cikin kungiyoyin kwararrun masu fida ta Afrika ta yamma da na Duniya, ya goge a harkar kula da cututtukan kashin kananan yara.
Bangaren da Adegbehingbe ya gwanance a kai shi ne maganin larurori a kafafun yaran.
Dr. Salman Ibrahim Anas ta fara aiki
Tun a shekarar bara ake ta faman rikici tsakanin shugabannin majalisar da ke sa ido da kuma shugabannin asibitin kan sha’anin shugabancin a OAUTHC.
Shugaban kungiyar likitocin asibitin, Farfesa Oluyomi Okunola ya yabi Dr. Salman Ibrahim Anas a kan yadda ta shawo kan wannan doguwar ja-in-jar.
Harkar wutar lantarki
Labari ya zo cewa a fara shiryawa tashin farashin lantarki daga tsakanin 25% zuwa 40% daga ranar 1 ga watan Yuli 2023 saboda hauhawar farashin kaya.
Da alama NERC za ta soke tallafin shan wutar lantarki a shekarar bana. Sannan sauyin da aka samu a kasuwar canji zai jawo karin tsadar lantarkin.
Asali: Legit.ng