“Ya Zama Dole FG Ta Daina Nada Ma’aikatan Banki a Matsayin Gwamnan CBN”, Dan Fafutuka Ga Tinubu
- An bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya guji nada wani ma'aikacin banki a matsayin gwamnan CBN bayan dakatar da Godwin Emefiele
- Deji Adeyanju, ya bayar da shawara a ranar Juma'a cewa ya kamata sabon gwamnan CBN ya zamo masanin tattalin arziki gogagge wanda ke da kwarewar aiki da kungiyoyi irin su IMF
- A cewar Adeyanji, ma'aikatan banki yan kasuwa ne kawai da basu san komai game da tafiyar da tattalin arzikin kasar ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
An shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da al'adar nan na nada ma'aikatan banki a matsayin gwamnonin babban bankin Najeriya (CBN), dadaddiyar al'adar babban bankin kasar.
Deji Adeyanju, wanda ya kasance dan fafutuka na Najeriya shine ya bayar da shawarar a wata wallafa da ya yi a Twitter a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni.
Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi
Yana martani ne ga shawarar da aka bayar cewa ya kamata Adesola Adeduntan, Shugaban bankin First Bank mai ci ya karbi mukamin gwamnan CBN.
Dalilin da yasa ya kamata Tinubu ya nada masanin tattalin arziki a matsayin gwamnan CBN
Adeyanju ya ba da shawarar cewa ya kamata Najeriya ta gwada nada masanin tattalin arziki mai gaskiya da gogewar aiki da kungiyoyin kasa da kasa irinsu IMF, yana mai cewa ma'aikatan banki yan kasuwa ne kawai da basu san komai game da tattalin arziki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shawarar na zuwa ne kimanin makonni biyu bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan CBN, kan zargin cin mutuncin ofis da daukar nauyin ta'addanci.
Shugaban kasa Tinubu ya dakatar da Emefiele ne kimanin mako guda bayan ya karbi rantsuwar kama aiki kuma nan take rundunar tsaron farin kaya wato DSS suka kama shi domin yi masa tambayoyi kan rashawa da zargin daukar nauyin ta'addanci.
Tun bayan dakatar da Emefiele, ana ta rade-radi da zuba idanu kan wanda shugaban kasar zai nada domin ya ja ragamar harkoki a babban bankin kasar kafin wallafar twitter da ya bayar da shawarar cewa ya kamata Adeduntan ya gaje shi.
Amma Adeyanju ya amsa da:
"Ya zama dole FG ta daina nada ma'aikatan banki a matsayin gwamnan CBN. Basu san komai game da tattalin arziki ba. Wadannan yan kasuwa ne kawai. Masanin tattalin arziki tare da kwarewar aiki da hukumomin kudi na duniya da kungiyoyi irinsu IMF, Bankin duniya da sauransu ne ya kamata ya zama gwamnan CBN.".
Kalli wallafar a kasa:
Godwin Emefiele: Jigon APC ya nemi Tinubu ya binciki Sanusi
A wani labari na daban, mun ji cewa jigon APC, Kailani Muhammad, ya shawarci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya isar da binciken da ake yi kan ofishin Godwin Emefiele har zuwa zamanin Sanusi Lamido.
Kailani ya nemi Tinubu da kada ya damu da ziyarar da tsohon sarkin Kanon ya kai masa, yana mai bayyana su a matsayin dabarun neman jan hankali.
Asali: Legit.ng