Cire Tallafin Man Fetur: FG Ta Fara Raba 'Solar' Kyauta A Fadin Ƙasar Don Rage Raɗaɗin Da Jama'a Ke Ciki
- Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara rabon na’urori masu amfani da hasken rana wato 'solar' kyauta a wasu yankuna na kasar
- Gwamnati ta ɗauki matakin ne domin rage raɗaɗin da jama'a ke ciki na cire tallafin da ta yi a baya-bayan nan
- Ana dai bayar da na'urorin na 'solar' ne kyauta domin a yi amfani da su a gidaje, asibitoci, kasuwanni da sauransu
Gwamnatin Najeriya ta fara rarraba na'urorin samar da wuta ta amfani da hasken rana (solar), a sassa daban-daban na ƙasar a kyauta don ragewa mutane raɗaɗin da cire tallafin man fetur da suke fama da shi.
Manajan daraktan Hukumar Samar Da Wutar Lantarki a Karkara (REA), Ahmad Salihjo, ne ya bayyana hakan.
Ya ce gwamnatin Najeriya ta umarci hukumar ta ƙara azama wajen kai ƙarin sololi zuwa gidaje, makarantu da asibitoci a fadin kasar nan.
Gwamnatin Tarayya za ta raba 'solar' kyauta don yaƙar talauci
Salihjo ya ce aikin na ƙarƙashin shirin ma’aikatar wutar lantarki na rage talauci da samar da ci gaba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ƙara da cewa, gwamnati ta lura da irin wahalhalun da ake ciki bayan cire tallafin man fetur da aka yi, musamman ma a yankunan karkara da ke fama da ƙarancin wutar lantarki.
Ya bayyana cewa a dalilin hakan ne suka zo da shirin, domin sanyawa ƙauyuka 'solar' mai ƙarfin aƙalla Watts 150, don amfani wajen haske, fankoki, da kallon talabijin.
Ahmad Salihjo ya kuma bayyana cewa akwai irin wannan sola sama da 30 da aka sanya a yankin Makoko da ke jihar Legas.
Ya ce mutanen da ke amfani da ita a yanzu sun gamsu sosai Da yadda suke samun biyan buƙatunsu, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Sannan ya ƙara da cewa gwamnati za ta ƙaro kuɗaɗe masu yawa domin a ci gaba da gudanar da shirin.
Sannan ya ƙara da cewa hukumar ta ziyarci Ijebu-Ode da ke jihar Ogun da kuma Osogbo a jihar Osun, inda aka sanya na’urorin na 'solar' a kasuwanni da wuraren noma.
Hukumar tana karɓar kuɗaɗe don sanyawa a wuraren kasuwanci
A cewar Salihjo, hukumar ta karɓi kuɗaɗe domin sanyawa a kasuwanni da wuraren noma a Ijebu da Osogbo. Sai dai ya tabbatar da cewa waɗanda aka sanya a gidaje, asibitoci, da makarantu an sanya su ne a kyauta.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Salihjo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci unguwar Makoko da ke Legas, inda shugaban yankin Migbewe 2, Cif Jeje Albert, ya ce al’ummar yankin sun yi farin ciki da gagarumin aikin.
An Bukaci Tinubu ya ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N200,000
A wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta cewa wata ƙungiyar ma'aikata, WAISER, ta nemi shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ɗaga mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati zuwa N200,000.
Kiran dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da ƙorafe-ƙorafe kan tallafin man fetur da shugaban ya cire.
Asali: Legit.ng