NNPCL Ya Gagara Kawo Sisin Kobo Duk da Cire Tallafin Fetur, Tinubu Ya Dauki Mataki

NNPCL Ya Gagara Kawo Sisin Kobo Duk da Cire Tallafin Fetur, Tinubu Ya Dauki Mataki

  • Ana kyautata zaton Bola Ahmed Tinubu ya nada kwamiti da zai binciki gaskiyar ayyukan NNPCL
  • An dauki tsawon lokaci ba tare da kamfanin man ya zuba kudi a cikin asusun hadaka na FAAC ba
  • Shugabannin NNPCL su ka rubuta takarda ga Tinubu, su ka bukaci ya binciki gaskiyar lamarin

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamitin cikin gida da zai duba sabanin da ake samu tsakanin kamfanin NNPCL da kwamitin FAAC.

Rahoto ya fito daga The Cable cewa shugaban kasa ya amince da wata takarda daga NNPC Limited domin abin da ya jawo kamfanin bai sa kudi a asusun FAAC.

Wata majiya ta tabbatar da NNPCL ta bukaci a gudanar da bincike na musamman domin gano hakikanin abin da ya sa kamfanin bai kawo kudi duk wata.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Aike da Sako Ga Tinubu, Ya Nemi Ya Binciko Badakalar CBN Tun Lokacin Sanusi

Tinubu
Shugaban Najeriya wajen taro da bankin AFREXIM Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Majiya ta ce za ayi bincike

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Hankali-kwance zan iya fada maka cewa Mai girma shugaban kasa ya amince da takardar NNPCL na kafa kwamitin binciken rikicinsa da FAAC.
Wasu manya sun fadawa Shugaban kasa abubuwa da-dama tun da ya shiga ofis cewa NNPC Limited ya ki sa kudi a cikin asusun tarayya.
Saboda ana so a san gaskiyar lamarin, shugabannin NNPC Limited sun rubutawa Shugaban kasa takarda domin ya yi bincike game da lamarin.
Mai girma shugaban kasa ya yi na’am da hakan, ya kafa wani kwamiti domin ya yi bincike a kai."

- Majiya

NNPC na bin Gwamnati bashin N2.4tr

Kamfanin man ya na ikirarin ya na bin gwamnatin tarayya bashin fiye da Naira tiriliyan 2.4 a sakamakon tallafin fetur, wutar lantarki da sauransu.

Leadership ta ce kwamitin zai fara yin zama ranar Juma’a a ma’aikatar tattalin arziki a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Nada Kwamiti, Za a Binciki Shekaru 4 da Tsohon Gwamna Ya Yi

‘Yan kwamitin sun hada da ma’aikatar tattalin arziki, hukumomin NUPRC da FIRS. Sannan akwai ofishin bmai binciken kudi na kasa (OAGF) da FAAC.

A labarin da aka samu daga The Guardian, an ji cewa a halin yanzu $473,754.57 ne a cikin asusun ECA da gwamnatin tarayya ta ke tara duk rarar kudin mai.

Har zuwa karshen watan nan, kamfanin mai na kasa watau NNPCL bai bada gudumuwar kobo cikin asusun hadaka ba duk da janye tallafin fetur.

Bashi zai yi katutu

Gwamnati ta shiga matsala har ta kai DMO ta gargadi Bola Tinubu game da karbo aron kudi a gida ko waje. Dazu mu ka fitar da wannan rahoto a shafinmu.

Hukuma ta ce bashin da ke kan wuyan Najeriya a yanzu ya yi yawa, dole a nemi hanyar samun kudi. Bashin kasar ya na nema ya kai Naira Tiriliyan 81.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng